Likitan Japan ya mutu a harin ta'addanci
December 4, 2019Sanarwar da fadar gwamnatin kasar ta Afghanistan ta fitar, ta nuna takaici kan mutuwar babban jami'in da asalin kasar Japan da kuma wasu mutum biyar da suka halaka a harin na wannan Laraba. Nakamura shi ne shigaban kungiyar agaji ta Japan da ke da reshe a Afghanistan, ya kwashi fiye da shekaru talatin yana tallafawa majinyata a kasashen Afghanistan da Pakistan kafin ya gamu da ajalinsa.
Mai magana da yawun shugaban kasar Sediq Seddiqi, ya baiyana likitan dan shekaru 73 da haihuwa, a matsayin jarumi kuma aminin Afghanistan da ya jefa rayuwarsa cikin hadari don ganin ya ceto rayukan al'umma musanman marasa galihu a kasar da ke ci gaba da fama da tashe-tashen hankula.
Kungiyar Taliban da ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare a kasar, ta nesanta kanta da harin, inda ta ce fadan da take yi bai shafi kungiyyoyi agaji ba saboda haka bata da hannu a kisan Nakamura. An dai kai hari kan tawagar likitan inda shi da wasu masu aikin kare shi da kuma direbansa suka halaka.