1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

London a yau jumma´a bayan hare haren jiya

Zainab A MohammadJuly 8, 2005

Harkoki sun kankama a London yau jumma´a

https://p.dw.com/p/Bvau
Hoto: AP
Wayewan garin yau a birnin London na kasar Britania dai ,jamaa na dari darin shiga ababan hawa ,musamman bus bus da jiragen kasa na pasinjoji sakamakon hare haren da suka ritsa da masanaantar sufuri jiya,wanda ya zuwa yanzu ya haddasa mutuwan mutane hamsim,banda daruruwa da suka jikkata.

Ayayinda wasu ke jin tsoron shiga bus bus dake daukan pasinjoji a cikin gari,wasu na hararan yan uwansu pasinjoji ,musamman wadanda ke dauke da jakunkunan kaya,bias ga zargin cewa harin jiyan na iya kasancewa kunar bakin wake.

A jiyan dai wasu pasinjoji dake shiga bus mai lamba 30,wadda wannan harin ya ritsa da ita,sun bayyana cewa sun ga wani mutum,wanda shekarunsa bazasu wuce 25 ba yana neman wani abu acikin jakarsa,inda dakikai kalilan bayan nan ne wannan ,aka samu fashewan wadannan ababai masu kama da boma baomai.

Daya daga cikin Pasinjojin da suka tsira da rayukansu Richard Jones ya fadawa Manama labaru cewa yaga lokacinda mutumin ya sanya hannu cikin jakarda yake dauke da ita,kuma bias dukkan alamu mutumin bad an kasar ta britania bane.

Gidajen talabijin sun nuna yadda jinin wadanda harin ya ritsa dasu a wannan bus ya bata gine gine dake kusa da titin,harin daya auku mintuna 56 bayan na farko daga cikin uku da suka ritsa da tashoshin karkashin kasa na jiragen kasa a jiyan a birnin London.

Idan dai har aka tabbatar da hare haren da kasancewa kunar bakin wake ne,wannan zai zame karo na farko irin wannan harin a nan nahiyar turai .

Yau jumaa dai harkoki sun kankama birnin na London,sai dai yansanda na cigaba da shiga bututun hanyoyin karkashin kasa na jiragen kasa domin neman shaida da sauran gawawwakin mutane da hare haren na jiya ya ritsadau,harin da ake zargin alqaeda da aiwatarwa.

Hare haren da suka ritsa da jiragen karkashin kasa uku da da Bus guda ,wanda ministocin kasar sukace yana nasaba da alamun kungiyar ta alqaeda ,na mai kasancewa abu mafi muni daya ritsa da birnin na London alokacin da akecikin kwanciyan hankali,harin da kuma a hannu guda ya girgiza taron kasashe masu cigaban masanaantu a duniya watau G8,wanda ke gudana a Gleneagles din Scotland.

Commandan rundunar yansanda na London Ian Blair yace sama da mutane 50 suka rasa rayukansu a yayinda kimanin 700 suka jikkata,ya kara dacewa har yanzu babu tabbaci dangane da Karin wadanda suka rasa rayukansu a hare haren na jiya.Domin yansanda na cigaba da binciken gawawaki a karkashin kasa.

Ayayinda jamiin yansanda dake lura da shiyyan Sufuri Andy Trotter yace babu tabbacin adadin gawawwaki dake makale a karkashin kasa,amma majiyar yansanda tace akalla zasu wuce na mutane 10.Mr trotter ya kara dacewa lokacin da harin ya auku lokaci ne da ake samun cunkoson jammaa acikin ababan hawa.

Yan sanda dai sun sanar dacewa basu samu wani gargadi ko kuma barazana gabannin wadannan harin na jiya ba,Sakataren harkokin cikin gida na Britania Charles Clarke ya bayyana harin da kasancewa abun mamaki ne garesu.

Jaridar newyork times ta bayyana cewa anyi amfani da naurori ne wajen tayar da boma boman akan lokaci amma ba kunar bakin wake ba,ayayinda shi kuwa Mr Blair ya jaddada cewa babu wata alama datayi nuni dacewa hare haren ,kunar bakin wake ne.

Wata kungiya dake kiran kanta Organisation of al qaeda,jihad in Arabian peninsula ,ta yanar gizo gizo ta Internet ta yabawa wadannan hara haren a jiya,tare da Karin bayanin cewa yanzu birnin Rome na kasar Italiya shine wuri na gaba.

Ayayinda hukumar kare hakkin dan adam ta shiyyan musulmi ta garghadi musulmi dake London dasu kasance a gidajensu ,domin gudun martanin alummomi akansu,kana majalisar musulmi mai wakililcin alumman musulmi milliomn1 da dubu dari 6 dake Britani,tayi kira dangane da adduoi wa wadanda harin ya ritsa da rayukansu.