Shugabannin NATO na ganawa a London
December 3, 2019Talla
Sai dai kuma a wani abun da zai zama tamkar gwaji ne ga shugabannin kasashe 29 mambobin kungiyar ta NATO, yayin wannan zaman za su tattauna yadda huldarsu da Rasha makomarta zai kasance, da kuma duba tasirin kasar a harkokin tsaron duniya.
Duk da wannan batu na Rasha, shugabannin kungiyar tuni suka hallara a birnin London don bikin cikar kungiyar shekaru 70 da kafuwa. Babban abin da zai kankane taron ana saran ya zama batun kasafin kudin tafiyar da kungiyar.
Batun rundunar NATO a Afganistan shi ma na daga cikin abin da kan iya zama muhawara mai zafi, yayinda kasar Jamus ke kokarin ganin an tsawaita wa'adin dakarun NATO a Kabul, Amirka kuwa na cewa shiri ya kamalla na fidda sojojinta daga Afganistan.