Luis Moreno Ocampo ya fara bincike a Kenya
May 8, 2010Babban mai gabatar da ƙara a kotun ƙasa da ƙasa dake hukunta masu aikata manyan laifuka, wadda ke birnin The Hague Luis Moreno - Ocampo, ya fara gudanar da binciken gano mutanen dake da hannu ta´asar da ta biyo bayan zaɓukan ƙasar Kenya a tsakanin 2007 zuwa 2008, inda kimanin mutane 1200 ne suka mutu, sannan wasu dubunnai suka shiga halin gudun hijira
Ocampo wanda a halin yanzu ke ƙasar ta Kenya domin bincike, ya bayyana cewar, hukunta waɗanda ke da hannu wajen cin zarafin mutane, tamkar aba gawa kashi ne domin mai rai ya ji tsoro, ya kuma cigaba da cewa:
Manyan laifuka ne aka tafka anan. Mutane da dama aka kashe, da yiwa wasu fyaɗe, kana da ƙona gidajen wasu. Dole ne in gudanar da binciken mai zurfi, domin gano hujjojin da zasu tabbatar da wanda ke da alhakin aikata ta´asar.
Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Halima Balaraba Abbas