Ma'aikata a tashar nukiliyar Fukushima na shirin ƙauracewa
March 23, 2011Ma'aikata a tashar nukiliyar Fukushima, sun ce za su ƙaurace bayan da wani baƙin hayaƙi daga ɗaya daga cikin tukwanen ya turnuƙe sararin sama. A yanzu haka dai tururin da ke sashi na biyu ya fara kai matakin da ke da hatsari kuma yawan zafin sashin farkon yana ƙaruwa. A yanzu haka dai sashi na huɗun ne kawai bashi da wani matsala bayan da aka sanyaya shi da ruwan teku.
Amurka ce ƙasa ta farko da ta hana shigar da madara da 'ya'yan itace da ganyayyakin da ake nomawa a yankin Fukushima, sakamakon fargabar tururin da ake zargin ya gurɓata amfanin gonan yankin. Gwamnatin Japan ta ce asarar da girgizar ƙasa da Igiyar ruwan tsunamin da ya afku a wannan watan ya janyo mata zai wuce dalan Amurka milliyan dubu ɗari ukku. Ɗaruruwan mutane na zaune a sansanonin wucin gadin da aka gigina musu a arewa maso gabashin Japan.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Ahmad Tijani Lawal