1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a hadarin jirgin kasa a Pakistan

Mouhamadou Awal Balarabe
June 8, 2021

Bayan mummunan hadarin jirgin kasa a kudancin kasar Pakistan, adadin wadanda suka rasa rayukansu ya haura 60 yayin da akalla mutane 150 suka ji rauni.

https://p.dw.com/p/3uasT
Weltspiegel 08.06.2021 | Pakistan Daharki | Zugunglück
Hoto: Asif Hassan/AFP/Getty Images

Hukumomin kasar Pakistan sun nunar da cewa adadin wadanda suka mutu a hadarin jirgin kasa na iya karuwa saboda da yawa daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali. A ranar Litinin ne wani jirgin kasa na fasinja ya ci karo da wani jirgin da ya kauce wa hanya a kusa da garin Daharki a lardin Sindh.

Kimanin mutane dubu da 200 ne ke cikin jiragen biyu da suka ci karo da juna. Sai dai hadarin jirgin kasa dai na neman zama ruwan are a kasar Pakistan, sakamakon rashin sabunta layin dogo da rashin kyakkyawar tsari na tafiyar da sufurin jiragen kasa.