Mace-mace a Kenya duk da matakan tsaron da aka dauka
March 4, 2013Tun da sassafe 'yan Kenya suka yi dogayen layuka domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasar na farko tun bayan wanda aka yi shekaru biyar da suka gabata, wanda ya jefa ƙasar cikin wani yanyi na yaƙi da tashe-tashen hankula. A yanzu haka dai hankula sun karkata ga wannan zaɓe wanda akewa kallon zakarar gwajin dafi ga ƙasar wacce shugabaninta suka yi alƙawarin cewa a wannan karon za'a yi zaɓen cikin kwanciyar hankali.
Tun ƙarfe huɗu na asuba, sao'i biyu kafin buɗe runfunan zaɓe waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a suka fara hallara suna shiga layi dan cika wannan tanadi wanda kundin tsarin mulki ya yi musu. Mutane d azama sun zauna a cikin wani yanayi na fargaba musamman a garin Mombasa inda aka hallaka 'yan sanda shidda a hare-hare daban-daban guda biyu, har ma da wata ƙofar ragon da wasu matasa suka yi wa jami'an tsaron jim kaɗan kafin buɗe runfunan zaɓen.
Yanayin da aka gudanar da zaben
To sai dai duk da haka Alojz Peterle shugaban tawagar ƙungiyar Tarayyar Turai da ke sanya ido a zaɓen a mazaɓar Dagoretti da ke wani makarantar Firamari a kudancin Nairobi ya ce ya gamsu da abunda ya gani kawo yanzu
"Yawancin runfunan zaɓen sun buɗe a kan lokaci, mutane sun fito ƙwan su da ƙwarƙwatarsu. Kuma mutane suna zaɓe cikin kwanciyar hankali babu gaggawa. Ko da ashike akwai matsalolin da ake samu da nau'rar ganin sunayen masu zaɓe, to amma akwai wani tanadin, inda ake amfani da takarda da biro a rubuta"
'Yan Kenyan na jefa ƙuri'u shidda, wadanda suka haɗa da na shugaban ƙasa, na 'yan majalisar dokoki, gwamnoni, majalisar dattawa, kansiloli da kuma wakiliya ta musamman na mata. mutane fiye da dubu 99 suka cancanci kaɗa ƙuri'a a runfunan zaɓe dubu 30 dake duk faɗin ƙasar.
Rawar kafofin yada labarai wajen kwantar da hankulan masu zabe
Kafofin yaɗa labarai sun taka rawar gani sosai wajen gabatar da shirye-shiryen da ke Allah wadai da rikicin da aka yi a shekarar 2008 wanda kuma suka riƙa yaɗa ƙasidun da ke cewa ko ɗaya bai kamata a maimaita ba. Mr Peterle ya ce bisa abubuwan da yake gani mutane sun amince da waɗannan shawarwarin:
"Daga abunda na ke gani da kai na a nan, fata na shine irin wannan yaynayi na wannan rufan zaɓe ya kasance a duk faɗin ƙasar, jami'an hukumar zaɓen sun tsara komai yadda ya kamata. to sai dai muna takaicin rahotannin tashe-tashen hankulan da suka afku a wasu wurare, amma kuma fatanmu shine kada su yaɗu zuwa sauran wurare su tsaya a can inda suka faru"
Manyan 'yan takaran shugaban ƙasa Frime Minista Raila Odinga da Uhuru Kenyatta sun fito fili sun yi alƙawarin cewa ba za'a samu maimaicin abunda ya faru a baya ba. Shari'ar manyan laifukan yaƙin da za'a ƙaddamar a Kotun ICC da ke Hague a kan ɗan takara Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto ya ƙara takarar kasancewar idan har suka lashe wannan zaɓen, zasu yi shekaru basu fuskanci shari'a ba.
Kuma a yanzu haka, manyan 'yan takaran biyu duk sun bada gaskiyar cewa zasu lashe zaɓen da rinjayen da ake buƙata ta yadda ba sai an shiga zagaye na biyu ba.
Wannan ɗaya daga cikin masu zaɓe ne wanda ya shi ma ya tofa albarkacin bakinsa dangane da wannan zaɓe:
"Nagode Allah babu waɗanda ke faɗa, ko kuma waɗanda ke suka, daga sun yi zaɓe suke komawa gida akwai banbanci sosai daga wanda aka yi a baya domin a wancan lokacin an yi abubuwa da dama da suka janyo ruɗani"
Martanin masu sanya ido daga kasashen ketare
To sai dai shugaban tawagar da ke sanya ido daga ƙungiyar Tarayyar Turai Mr Peterle ya ce babban ƙalubalen da yake hange na wajen hukumar zaɓen
"babu shakka babban ƙalubale ne a gudanar da zaɓuka shidda a lokaci guda, amma kuma muna ganin ma'aikata waɗanda suka bada kansu wajen ganin cewa sun yi aiki tuƙuru wajen ganin sun shawo kan waɗannan matsaloli saboda haka muna fatan ganin sun kammala wannan zaɓe lami lafiya.
rikicin da aka yi a shekarar 2008 ya kawo rarrabuwa sosai a tsakanin al'ummomin Kenya sosai amma kuma a wannan karon hukumomin sun ce sun ɗauki matakan da zasu rage maguɗin zaɓe
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammed Awal Balarabe