1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafaka ga 'yan gudun hijirar Siriya a Jamus

September 9, 2013

Bisa cike wasu ka'idoji da aka gindaya, tarayyar Jamus za ta dauki 'yan gudun hijira kimanin 5,000 daga Siriya, don ba su mafaka ta wucin gadi a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/19eBj
Der Krieg in Syrien und die Folgen für Libanon: Flüchtlingslager in Tripoli. Copyright: DW/Ibrahim Chaloub
Hoto: DW/I. Chaloub

Fiye da shekaru biyu ke nan ake gwabza yakin basasa a Siriya tsakanin dakarun shugaba Bashar al-Assad da masu adawa da gwamnati. Fararen hula ne dai suka fi jin jiki a wannan mummunan rikici, inda sama da mutane miliyan biyu suka tsere daga kasar. Wasu daga cikinsu kuwa sun samu mafaka a tarayyar Jamus, karkashin wani shirin Jamus na daukar wani kaso na 'yan gudun hijira daga kasar ta Siriya.

Bisa bayanan da ministan cikin gidan Jamus Hans-Peter Friedrich ya bayar a cikin watan Maris, a ranar Laraba rukunin farko na 'yan gudun hijirar su kimanin 5,000 daga Siriya za su fara isowa tarayyar ta Jamus.

Ka'idojin zaban 'yan gudun hijira

Mai magana da yawun ministan cikin gidan ta ce an zabi wadanda suka cancanci shigowa Jamus ne bayan wasu shawarwari tsakanin ministan da Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da kuma kungiyoyin agaji. An zabi mutanen su 5,000 daga rukunan 'yan gudun hijirar da suka tsere zuwa Lebanon. Kungiyoyin agaji sun yi rajistar 'Yan gudun hijirar Siriya fiye da 700,000 a makwabciyar kasar wato Lebanon. Stefan Telöken shi ne kakakin Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD yayi karin haske kan hanyoyin da ma'akatansa ke bi wajen tantance 'yan gudun hijirar.

Irakische Flüchtlinge stehen am 09.10.2012 am Flughafen Hannover neben dem Flugzeug. Deutschlands Bundesinnenminister Hans-Peter Friedrich (CSU - l) nahm die Iraker in Empfang. Bis 2014 will Deutschland 900 besonders schutzbedürftige Flüchtlinge aus Krisenregionen aufnehmen. Foto: Holger Hollemann/dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++
Ministan cikin gida Friedrich yana tarbar 'yan gudun hijirar Iraki a HannoverHoto: picture-alliance/dpa

"Suna neman bayanai daga takardun rajistar 'yan gudun hijirar, suna tuntubar wadanda abin ya shafa su tambayesu ko suna son zuwa Jamus. Sai dai wannan ba shiri ne na sake tsugunar da su ba."

An fi mayar da hankali kan batutuwa guda uku da suka hada da na jin kai alal misali masu rauni mai tsanani ko marayu ko iyaye mata dake renon yara su kadai. Hakazalika 'yan gudun hijirar da ke da 'yan uwa a Jamus ko suka iya Jamusanci na uku sai masu kwarewa a wata sana'a wadanda za su iya ba da gudunmawar sake gina kasar bayan yakin. Duk wanda aka zaba ta wannan hanya za a ba shi izinin zama da kuma aiki a Jamus tsawon shekaru biyu, wato na ba sa cikin rukunin masu neman mafakar siyasa.

Zangon farko a Friedland

Da farko za a tsugunar da 'yan Siriyar 5,000 tsawon makonni biyu a wasu sansanonin kan iyaka a Friedland da kuma Bramsche inda za a shirya su ga zaman da za su yi a Jamus.

Ein irakischer Flüchtling geht am 25.07.2012 im Grenzdurchgangslager Friedland (Niedersachsen) an einer Unterkunft vorbei. Anfang September rechnet das niedersächsische Innenministerium frühestens mit der Ankunft der ersten syrischen Flüchtlinge auf dem Flughafen Langenhagen. Foto: Swen Pförtner/dpa (zu lni "Niedersachsen rechnet ab September mit ersten syrischen Flüchtlingen" ***FREI FÜR SOCIAL MEDIA***
Sansanin 'yan gudun hijira a FriedlandHoto: picture-alliance/dpa

Heinrich Hörnschemeyer shi ne mai daraktan sansanin Friedland ya yi wa DW karin bayani.

"Tsawon mako guda za su yi kwas na radin kai. Da safe za a yi kokarin koya musu harshen Jamusanci, inda a karshen makon za su iya gabatar da kansu ko neman bayanan iya gwagwado. Da rana za su yi kwas na samun karin bayani game da tarayyar Jamus."

Yawan 'yan gudun hijirar da ko wace jiha daga cikin 16 na tarayyar Jamus za ta dauka ya danganci yawan al'ummarta. Sai dai Bernd Mesovic matamakin daraktan kungiyar tallafa wa 'yan gudun hijira a Jamus ta Pro Asyl ya ce yawan 'yan gudun hijirar 5,000 daga Siriya yayi kadan.

"Idan aka yi la'akari da mawuyacin halin da 'yan gudun hijira Gabas Ta Tsakiya ke ciki, to wannan adadi bai isa ba. Kuma wadanda aka yi wa rajista a matsayin masu neman kariya a Lebanon za a dauka."

Kungiyar ta Pro Asyl ta kara da cewa wannan shiri na daukar 'yan gudun hijirar bai ba da la'akari ga dubban mutane dake cikin halin ni 'ya su ba.

Mawallafa: Carla Bleiker / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe