Mahajjata na hawan Arfa
September 11, 2016Talla
Yayin wannan tsaiwa dai alhazan za su shafe wunin yau suna salloli da zikiri da addu'o'i. Tun a ranar Juma'ar da ta gabata ce wasu mahajjatan suka fara tafiya Muna domin yin tsayuwar Arfa din a yau. A bana ne dai aka cika shekara guda bayan da aka gamu da wani ibtila'i na rasuwar dubban Alhazai sakamakon wani turmutsutsu. Sai dai a wannan karo hukumomi a Saudiyya din sun ce sun dauki dukkanin matakan da suka kamata domin kauracewa matsalar da ta auku a bara wadda ita ce mafi muni da aka gani a tarihin aikin hajji na baya-bayan nan.