1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahama ya fito da tsarin bunkasa noman cocoa a Ghana

December 16, 2024

Zababben shugaban Ghana John Dramani Mahama ya sha alwashin habbaka noman cocoa tare da kawo sauye-sauye a hukumar da ke kula da kasuwancinsa a wannan kasa da ke zama ta biyu mafi girma a wajen noman cocoan a duniya.

https://p.dw.com/p/4oCUO
Hoto: Seth/Xinhua/IMAGO

A yayin wata hira ta musamman da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Mr. Mahama, ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da noman cocoan a hukumance, yana mai sukar hukumar COCOBOD wadda ke kayyade farashin kayan gonar da cewa jami'anta na gogayya da manoma wajen neman riba.

Sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 7 ga watan Disambar ne dai ya bai wa  John Dramani Mahama gagarumin rinjaye bayan korafin tsadar rayuwa da komabaya da 'yan kasar suka ce suna fuskanta a wajen noman cocoa da hakar ma'adanai.A ranar 7 ga watan Janairu mai kamawa ne dai ake sa ran za a rantsar da tsohon shugaban kasar ta Ghana a karo na biyu, kuma babban aikin da ke gabansa shi ne bunkasa tattalin arzikin jama'ar kasar da ya ragargaje a hannun gwamnatin jam'iyya mai mulkin kasar.