Mahukuntan Kenya sun kai samame wurin yin barasa
July 4, 2015Mutane takwas sun hallaka, wasu da dama kuma sun yi rauni sakamakon wani samamen da mahukuntan Kenya suka kai wani wurin da ake yin barasa ba bisa ka'ida ba. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa an kama daruruwan mutane an kuma lalata wasu shagunan masu sana'o'i da dama, sanan an zubar da dubban litoci na barasan.
Mahukuntan sun kai samamen ne yankunan da ke tsakiyar Kenya, da babban birnin kasar wato Nairobi inda akalla mutane 80 suka rasu a yayin da wasu da dama kuma suka makance a dalilin wani sinadarin da aka sanya a cikin barasan mai suna Methanol, wanda akan yi amfani da shi ne don hana abubuwa daskarewa a cikin kankara.
Wata jarida mai suna The Star ta ce mutane bakwai daga cikin takwas din sun mutu a cikin wata mota da ke dauke da barasar da aka kwato, inda ake zargi daya daga cikinsu ne ya kunna ashana, a yayinda aka harbe dayan lokacin samamen.