1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maiduguri: Matashiya makauniya mai yin sana'a

December 18, 2019

Falmata Muktari wata matashiya ce mai lalurar rashin gani amma hakan bai sa ta kashe zuciyarta ba ta shiga yin bara maimakon haka ta rungumi sana’ar sarrafa sabulai.

https://p.dw.com/p/3V0j3
DW Eco@africa - Eco-soap
Hoto: DW

Ita dai Falmata Muktari na daga cikin masu fama da nakasa amma suke ganin ba nakasashe sai kasashe kuma duk abin da mai lafiya zai yi ita ma za ta yi bakin kokarin na ganin ta yi sai dai abin da ya fi karfinta. Bisa wannan tunani da take da shi ne ya sa ta nemi wurin da ake koyon sana’o’i inda ta je ofishin Damna’ish ta shafe lokaci ta koyi yadda ake sarrafa sabulai na ruwa da kuma wanda ake wanki da shi da kuma man shafawa. Falmata Muktari ta bayyana dalilanta na koyon wannan sana’a a daidai lokacin da wasu tsaranta masu lafiya ke zaman kashe wando ko kuma kashe zuciya suna bara.