1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maiduguri: 'Yan gudun hijira sun gurfana a kotu

Salissou Boukari
September 26, 2017

Wasu mutane 10 da ake zagi da shirya zanga-zangar 'yan gudun hijira a Maiduguri a Arewa maso gabashin Najeriya sun gurfana a gaban kotun Wulari da ke Maigurin, inda ake zarginsu da neman tayar da zaune tsaye.

https://p.dw.com/p/2klac
Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Hoto: Reuters/S.Ini

Wani jami'in ma'aikatar shari'ar ta Maiduguri da bai so a bayyana sunan shi ba, ya ce an gabatar da mutanen ne cikin gaggawa a gaban alkali cikin mataki na tsaro, inda kuma ya ce daga cikinsu babu wanda ya amsa laifinsa ko kuma akasin haka, sannan alkalin ya bada izinin a ci gaba da tsare su har zuwa ranar 23 ga watan Oktoba mai zuwa lokacin da za a yi mu su shari'a.

Wadannan mutane 10 dai an kama su ne daga cikin 'yan gudun hijira 3000 da ke sansanin 'yan gudun hijira na Dalori da suka yi zanga-zanga a ranar Lahadi don neman a kyautata halin rayuwarsu, ko kuma a mayar da su zuwa garinsu na Bama da ke nisan kilo-mita 70 da inda sansanin na su yake. Daga cikin mutanen da aka kama har da shugaban kungiyar matasan Bama wanda ya nemi da a yi masa sakin talala amma kuma kotun ta ki amincewa.