1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Majalisa ta amince da dage zabe

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 6, 2024

Rahotanni daga Senegal na nuni da cewa mafi rinjayen 'yan majalisun dokokin kasar, sun amince da matakin dage zabe da Shugaba Macky Sall ya dauka.

https://p.dw.com/p/4c6oC
Senegal | Macky Sall | Shugaban Kasa
Shugaba Macky Sall na SenegalHoto: RTS/Reuters

Bayan wata zazzafar muhawara da mambobin majalisar dokokin Senegal din 165 suka fafafata, 105 daga cikinsu sun amince da dage zaben shugaban kasa zuwa ranar 15 ga watan Disambar bana. Tun da fari dai an tsara gudanar da zaben shugaban kasa a Senegal din, a ranar 23 ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki. Matakin dage zaben da Shugaba Macky Sall ya dauka na ba-zata ya janyo zanga-zanga a kasar a karshen mako, inda jami'an 'yansanda suka murkushe ta da karfin tuwo. 'Yan majalisar dokokin kasar na bangaren adawa, sun bayyana matakin dage zaben da juyin mulki. Su kuwa wakilan kungiyoyin Tarayyar Turai EU da Tarayyar Afirka AU da kuma na kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, sun bayyana damuwarsu ne kan matakin na Shugaba Sall na Senegal.