Majalisar Faransa za ta kawar da firaministan kasar
December 3, 2024A wannan Laraba mai zuwa ake sa ran 'yan majalisun kasar Faransa za su kada kuri'ar yanke kauna ga gwamnatin Firaminista Michel Barnier sakamakon rikicin siyasa da kasar, wadda ke zama ta biyu mafi karfin tattalin arziki tsakanin kasashen kungiyar Tarayyar Turai. Muddun aka yanke kauna ga Barnier, hakan zai zama karon farko cikin fiye da shekaru 60 da aka kifar da wata gwamnatin da firaminista yake jagoranta.
Muddun aka kada wannan kuri'a ta yanke kauna kuma aka samu nasara tilas Firaminista Michel Barnier ya mika wa Shugaba Emmanuel Macron takardar ajiye aiki, sannan Banier zai ci gaba da rike mukamun na firaministan wucin gadi har zuwa lokacin da za a nada sabon firaminista zuwa sabuwar shekara ta 2025.
Wannan rikicin siyasar Faransa na zuwa lokacin da kasa mafi karfin tattalin arziki tsakanin kasashen Turai, wato Jamus aka shiga yanayin zabe bayan rushewar gwamnatin hadakar kasar, kuma makonnin kafin Donald Trump ya dauki madafun iko a matsayin sabon shugaban Amurka, wanda ya yi alkawarin kawo sauye-sauyen da za su tasiri game da dangantakar kasar da sauran kasashen duniya.