1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar ɗinkin duniya ta sanyawa Koriya ta arewa takunkumi

October 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bufs

Kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya ya zartar da ƙudiri ba tare da hamaiya ba na sanyawa Koriya ta arewa tsauraran takunkumi a sakamakon gwajin da ta yi na makaman nukiliya. Ƙudirin wanda ya ƙunshi takunkumin makamai dana karya tattalin arziki ya sami amincewar ɗaukacin wakilai goma sha biyar na kwamitin tsaron. Ɗaukar wannan mataki ya biyo bayan cimma masalaha tsakanin Amurka da Britaniya da Faransa bisa togaciyar da ƙasashen China da Rasha suka yi tun da farko na ƙin yarda da sanya takunkumin har ila ma sha Allahu. Jakadan Koriya ta arewa a Majalisar ɗinkin duniya Pak Gil Yon yace ƙasar sa ta yi Allah wadai da ƙudirin, yana mai cewa sun gudanar da gwajin makman ne bisa matsin lamba da ƙuntatawar da Amurka kewa ƙasar. Ƙundirin dai ya buƙaci Koriya ta arewa ta kawar da dukkan makaman ta na nukiliya ta kuma ƙaucewa dukkanin wasu gwaje gwaje a nan gaba. Da yake maida martani a game da ƙudirin shugaban Amurka George W Bush yace ɗaukar matakin ya nuna a fili cewa ƙasashen duniya kan su a haɗu wajen nuna adawa da burin Koriya ta arewa na mallakar makamin ƙare dangi.