Komi ya daidaita a Amirka
January 7, 2021Talla
Majalisar Dinkin Duniya gami da kasashe masu fada a ji a fadin duniya da suka hada da China da Jamus, sun bayyana abin da ya faru na afkawa harabar majalisar dokokin Amirka da wasu magoya bayan shugaba Donald Trump suka yi a matsayin karan tsaye ga demokaradiyya.
A kalla mutane hudu ne suka rasa rayukkansu cikinsu har da wata mata, inda kuma 'yan sanda suka chafke masu zanga-zanga sama da hamsin a arangamar da suka yi.
Kawo yanzu abubuwa sun fara daidaita a majalisar, kuma gaba kadan za a cigaba da shirin na tabbatarwa zababben shugaban kasar Joe Biden nasararsa.