Majalisar dattijan Amirka ta amince da shirin tsige Trump
February 10, 2021'Yan majalisa 56 suka kada kuriar amincewa yayin da 44 kuma suka ki amincewa da kudirin tsige tshon shugaba Trump. Ko da yake yawancin 'yan majalisar sun kada kuriar ce da muradun jam'iyyunsu, 'yan majalisa shidda na jam'iyyar Republican sun yi hannun riga da jam'iyyarsu inda suka kada kuri'ar amincewa da shirin tsige tshohon shugaban kasar Doanld Trump.
Sai dai har yanzu 'yan Democrats na da jan aiki a gaba na iya shawo kan karin 'yan majalisu 11 na Republican kafin su sami rinjaye don tsige tshohon shugaban. Trump yana fuskantar tuhuma ce kwaya daya na tunzura jama'a domin bijirewa gwamnati wanda 'yan Democrats suka ce Trump ne ya assasa gangamin. Sai dai Lauyan Trump Bruce Castro yace batun tsige Trump ba shi da wani tasiri saboda ya riga ya sauka daga karagar mulki.