Majalisar Dinkin Duniya na daukar matakai a Najeriya
November 18, 2016Majalisar Dinkin Duniya ta kudiri aniyar taimaka wa mutanen da suka rasa muhallansu a jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya, inda ta kara yawan ma'aikatanta a Maiduguri daga 40 zuwa 200. Wakilin musamman na sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kasashen Afrika ta yamma da yankin Sahel Mohammed Ibn Chambas ne ya bayyana haka a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar, a ganawar da ya yi da ministan yada labarai da ala'adun gargajiya na kasar a ranar Juma'a 18 ga watan Nuwamba 2016, inda ya bayyana irin yanayin da ya iske yankin, musamman halin da ‘yan gudun hijira ke ciki.
Mr Chambas ya ce a yanzu Majalisar Dinkin Duniyar ta fara sauya aikin nata daga na taimakon jin kai zuwa ga na sake farfado da yankunan da aka kwato daga hannun Boko Haram. Kimanin mutane miliyan 200 ne dai yakin na Boko Haram ya shafi rayuwarsu a yankin Tafkin Chadi.