1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman gaggawa a kan gwajin makaman Koriya ta Arewa

Kamaluddeen SaniJanuary 6, 2016

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na shirye-shiryen wani zaman gaggawa a ranar Larabar nan a birnin New York bayan da Koriya ta Arewa ta yi ikirarin aiwatar da gwajin makamanta.

https://p.dw.com/p/1HZF6
Nordkorea TV Berichterstattung Südkorea zu Wasserstoffbombe
Hoto: picture-alliance/AP Photo/L. Jin-man

Tattaunawar ta membobin kasashen kwamitin tsaron 15 na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasar Japan suka kira za su duba batun sarkakiyar da ta dabaibaye gwada makaman da Koriya ta Arewa ta yi ne.

A cewar mai magana da yawun Majalisar ta Dinkin Duniya Hagar Chemali, ba za su iya tabbatarwa ba a kan ko kasar ta aiwatar da gwajin. To amma sun yi Allah wadai da duk wata karya ka'ida da aka yi kana kuma suna kira ga Koriya ta Arewa da ta mutunta dokokin kasa da kasa.

Da dama dai kudurorin kwamitin tsaro ya sha haramta wa Koriyan ta Arewan aiwatar da duk wasu aikace-aikace a kan makaman nukiliya da kuma makamai masu linzami.