Majalisar dokokin Girka ta amince da shirin tsimin gwamnati
July 11, 2015Majalisar dokokin kasar Girka ta bada amannarta kan tsarin shawarwarin da gwamnatin kasar ta fitar wadanda za su kasance madogara a ci gaba da tattaunawar da kasar za ta yi da masu biyarta bashi da suka hada da Tarayyar Turai, da babban bankin Turai da kuma asusun bada lamuni na duniya wato IMF.
Sai dai duk da haka Firaministan na Girka Alexis Tsipras, ya fuskanci bijirewar wasu daga cikin 'yan majalisun na jam'iyyarsa ta Syriza akalla guda goma, inda biyu daga cikinsu suka kada kuri'ar kin amincewa, yayin da takwas kuma suka ce baruwansu.
Daga cikin takwas din da suka ce ba ruwansu, akwai ministoci biyu da kuma shugaban majalisar kanshi Zoe Konstantopoulou, da ke a matsayin na uku a kasar ta Girka. Ga baki daya dai 'yan majalisa 251 ne daga cikin 300 suka kada kuri'un amincewa da wannan tsari.
Tuni dai masu lura da al'amura ke ganin cewa, nokewar da wasu ministocin gwamnatin suka yi na iya janyo garambawul a majalisar ministocin kasar ta Girka.