1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Jamus ta tuna da barkewar yakin duniya na biyu

Mohammad Nasiru AwalSeptember 10, 2014

Zaman alhinin na daga cikin jerin bukukuwan da ake yi na tunawa da cika shekaru 75 da fara yakin, wanda ya janyo mummunan bala'i ga duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/1D9qw
Bundestag Generaldebatte 10.09.2014 Regierungsbank
Hoto: DW/K. Scholz

A wani zama da aka yi a wannan Laraba don nuna alhini da barkewar yakin duniya na biyu shekaru 75 da suka wuce, shugaban majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, Norbert Lammert ya yaba da kyakkyawar hulda tsakanin Jamus da Poland. Ya ce kasar Poland ce farkon da yakin duniya ya shafa wadda kuma ta kawashe tsawon lokaci tana karkashin mamayar Jamus.

"A yau muna nuna alhini ga mummunan yakin da ya auku a cikin tarihi. Yakin da Jamus ta haddasa, wanda kuma ya janyo mummunan bala'i ga al'umma."

Shi ma a jawabin da ya yi a gaban majalisar dokokin ta Jamus, shugaban Poland Bronislaw Komorowski tuni ya yi da cewa kwanaki kalilan bayan Jamus ta mamaye Poland a ranar daya ga watan Satumban shekarar 1939, sojoji Tarayyar Sobiet sun kutsa kasar.

"Ya zama dole mu tuna tare kuma da sanin cewa kowa ya ji jiki a yakin duniya na biyu. Ba kawai wadanda yakin ya shafa ba, har ma da 'yan kasashen da suka ta da wannan fitina."

Daga cikin wadanda suka halarci zaman nuna alhinin akwai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasa Joachim Gauck.