SiyasaTurai
Majalisar EU na shirin bai wa Von der Leyen damar zarcewa
January 26, 2024Talla
Wani babban jami'in Majalisar Tarayyar Turai ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, kawancen jam'iyyu masu ra'ayin mazan jiya za ta zabi Ursula von der Leyen a matsayin shugabar Hukumar Tarayyar Turai, idan har ta na muradin zarcewa a karo na biyu, a yayin taron jam'iyyun a watan Maris.
Von der Leyen 'yar jam'iyyar Christian Democrat ta Jamus, har yanzu ba ta fito fili ta bayyana ko tana son wa'adi na biyu na shugabancin kungiyar EU ba, bayan karewar wa'adinta na yanzu a karshen wannan shekarar.
Daniel Caspary, wanda ke jagorantar 'yan majalisar jam'iyyar ta Christian Democrat ta Jamus a majalisar dokokin Turai ya ce, yana sa ran jam'iyyar ta masu ra'ayin mazan jiya su sake zabarta ta.