140109 Dialog Gymnasium Köln
January 22, 2009An buɗe makarantar ce ga baƙi musamman Turkawa da Larabawa da nufin shirya su yadda za su tinkari buƙatun rayuwar yau da kullum a Jamus ba tare da sun yi watsi da asalinsu ba. Tun bayan kafa makarantar a bara yanzu haka dai akwai yara 37 waɗanda ke cikin azuzuwa biyu na shekarar farko ta karatu. Malamai bakwai ciki har da mai koyar da harshen Turkawa ke bawa yaran darasai. Babbar manufar kafa wannan makaranta dai ita ce bawa ´ya´yan baƙin musamman ´ya´yan musulmi, damar kammala sakandare. Wannan makarantar dai ba ta matsayin wata cibiyar yaɗa wani addini kuma ba ruwanta da harkokin siyasar duniya. To shirin Taɓa ka Lashe na wannan mako ya kai ziyara a wannan makaranta dake birnin Kolon.
Waɗannan dai yaran makarantar firamaren kenan mai zaman kanta ta birnin Kolon suna bayyana burinsu a rayuwa. Daga mai son ya zama injiniyan ƙera motoci sai masu son zama likitoci ko malamai ko masu aiki a ofis in sun girma. Dukkansu dai abu ɗaya ya haɗa su wato ba su da asali da Jamus amma suna amfani da takardun zama ´yan ƙasar ta Jamus. A dangane da haka ba dole ba ne makarantar ta tafiyar da wani aiki na nunawa yaran yadda za su yi cuɗanya da Jamusawa ba, inji shugaban makarantar Gregor Hohmann van Haaren.
“Ko da yake wannan makarantar tana da asali da baƙi to amma dukkan ´yan makarantar suna da fasfuna na Jamus wato kenan dukkansu Jamusawa ne. Shi ya sa ba dole ne mu ba su wani darasi na musamman ga yadda za su shaƙu da wannan al´uma ba. Abin da muka sa a gaba shi ne yadda za mu nuna musu ainihin halin da ake ciki a wannan ƙasa. Dole ne mu fita da yaran waje saboda haka a kullum ƙofar mu a buɗe ta ke ga duk mai muradin kawad da manufar nuna wariya a duniya baƙi ɗaya.”
´Yan makarantar dai na da masaniya musamman dangane da inganta fahimtar juna tsakanin al´umomi. Domin da yawa daga cikinsu suna rayuwa ne a cikin wata al´uma dake mayar da su saniyar ware. Kamar yadda wannan yaron ya nunar.
“Iyayen da yawa daga cikin ´yan makarantar ´yan ƙasashen waje ne alal misali kamar daga Iraqi ko wasu ƙasashen Larabawa. Ni kai na mahaifi na Balarabe ne. Amma a makarantar da nake a da, mun kasance saniyar ware domin mun fito daga ƙasashen ƙetare ne, amma a nan abubuwa sun bambamta. Malamanmu na da kirki, haka ma ´yan makaranta. A nan ba za mu taɓa saniyar ware ba.”
Yaran makarantar dai ba su da wata matsala ta fahimtar harshen Jamusanci. Ɗaukacinsu sun ƙware cikin harsuna biyu wato Jamusanci da kuma na asalinsu wato kamar Larabci da kuma harshen Turkawa. Saboda haka ake koyar da harshen Turkawa a makarantar amma a matsayin wani harshe na ƙetare inji Seyit Ahmed Tokmak daraktan makarantar.
“Abin da ya bambamta makarantarmu da saura shi ne ta na koyar da harsuna da yawa. To amma ina mai jaddada cewa da Jamusanci muke koyarwa. Harshen Ingilishi ne na farko a jerin harsunan ƙetare da suka wajaba a koya. Baya ga haka muna bawa ´yan aji daga na biyar damar zaɓi tsakanin Faransanci da kuma harshen Turkawa.”
Duk da haka dai da farko an nuna shakku game da kafa wannan makaranta wadda tarayyar masana ilimin jami´i ta Turkawa da Jamusawa ta ƙirƙiro. A da an nuna fargabar cewa makarantar mai zaman kanta ka iya zama mafarin buɗe jerin makarantu na ´yan Turkiya zalla a Jamus. Amma shugaban makarantar Hohmann van Haaren ya ce ba haka abin yake ba.
“Tarayyar masana ilimi ta Turkawa da Jamusawa ke ɗaukar nauyin tafiyar da wannan makaranta, amma a tsakanin jama´a ana yi mata kyallon wata makarantar Turkawa. Wannan babban kuskure ne. Makarantar ba ta Turkawa ba ce, makaranta ce ta Jamusawa mai bin tsarin koyarwa na Jamus. Sunan ƙungiyar dake tafiyar da ita ne ke haɗe da kalmar Turkiya.”
Adawar da jama´a suka nuna ga buɗe makarantar na da nasaba da shakkun da al´umar wannan ƙasa ke nunawa ga duk wani abu da ke da alaƙa da adinnin musulunci. To sai dai abubuwan da ´yan makarantar ke sha´awa musamman a dangane da fannonin karatu ya dace da sauran yara ´yan makaranta a tarayyar Jamus baki ɗaya. Hatta su kansu shugabanni da masu ɗaukar nauyin tafiyar da makarantar ba su damu da tarbiya ta wani addini ba. Burinsu shi ne bawa yaran darasi da ya dace da rayuwar wata ƙasa mai ƙunshe da al´umomin daban daban. A nan kuwa har da batun addini ko da yake ba ya taka wata rawar a zo a gani a manhajar koyarwa ta makarantar. Seyti Ahmed Tokmak daraktan makarantar ya ce suna aiki sau da ƙafa da dokokin koyarwa na jihar North Rhein Westfalia.
“E haka ne dole ne mu koyar da darussan addini kamar yadda dokar makaranta ta jihar North Rhein Westfalia ta tanada. Muna gabatar da darussan addini kamar na ɗarikar Katholika ko Evangelika muddin iyaye yaran da kuma yaran kansu sun nuna buƙatar haka. Ana iya zaɓan darussa na tarbiya.”
Haka batun addinin da ma sauran batutuwan suke game da koyarwa ta gari. Ana tattaunawa kan dokokin addini. Shugaban makarantar van Haaren yana adawa da duk wani umarni na sanya tufafi. Amma duk da haka yana girmama dokokin addinai.
“Ina iya cewa ni ba ma´abucin ɗan kwali ba ne. Domin a gareni alama ce ta dannen ´yancin mata, walwala da dai abubuwa masu yawa waɗanda ba su dace da yaranmu. To amma ba za mu hana yin lulluɓi ba. Ba zan taɓa hanawa wata yarinya ɗaura ɗan kwali ba. Haka yake ga malamai mata. To amam zan ci-gaba da neman yin muhawwara kan wannan batu. Na yi imani a ƙarshe gaskiya za ta bayyana.”
A halin nan da ake ciki dai addinin ba ya taka wata muhimmiyar rawa a rayuwar ´yan makarantar saɓanin yadda ake zato. Domin a lokacin hutu sun fi mayar da hankali kan wasu abubuwa daban wato kamar wasan ƙwallon ƙafa da kuma tenis.