1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar demokraɗiyya a Ghana bayan mutuwar shugabanta

July 26, 2012

Ghana wadda a ranar Talata ta yi rashin shugabanta, John Atta Mills ƙasa ce dake da kwanciyar hankalin siyasa da kyakkyawar zamantakewar al'umma.

https://p.dw.com/p/15exW

Ƙasar dake yankin yammacin Afirka na zaman wata abar koyi ga sauran ƙasashen Afirka musamman wajen girke kyakkyawan mulkin demokraɗiyya. Sai dai tambayar da ake ita ce ko ƙasar za ta ci-gaba da zama jagora bayan mutuwar shugabanta John Evans Atta Mills?

Ko shakka babu ƙasar Ghana na matsayin kyakkyawar abar koyi ga sauran ƙasashen yankin yammacin Afirka. Fannoni da dama na tattalin arzikinta suna da ƙarfi kuma suna ci-gaba da haɓaka. A fannin siyasa ma ƙasar tana bin kyakkyawan tsarin demokraɗiyya. Kuma duk da mutuwar ba zato ba tsammani ta shugabanta John Evans Atta Mills a ranar Talata, hakan ba za ta canza ba, inji Daniela Kuzu shugabar ofishin gidauniyar Friedrich-Ebert dake Accra babban birnin ƙasar ta Ghana, wadda har wa yau ta ayyana kyakkyawan fata ga shugaban wucin gadi kuma aminin marigayi da shugabanci na gari.

"Sun kasance masu kyakkyawar fahimtar juna kuma a suna tuntuɓar a kullum. A saboda yawan tafiye tafiyensa, John Atta Mills yayi ta sakar wa John Mahama ragamar mulkin ƙasar. Da yawa daga cikin 'yan ƙasar suna cewa shi ne ma yake mulki. Yayi aiki a fannoni da yawa, a saboda haka ana girmama shi kuma ya samu amincewa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa."

Ɓaraka a tsakanin 'ya'yan jam'iyar NDC

Kuzu ta yi ammanar cewa John Mahama zai tsaya wa jam'iyar NDC takara a zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana a cikin watan Disamba mai zuwa. Hakan kuwa ka iya zama wata alama ƙwaƙƙwara ga John Mahama wanda kirista ne daga arewacin ƙasar, domin bisa al'ada 'yan siyasa daga kudu suka mamaye fagen siyasar ƙasar ta Ghana. Sai dai ba a sani ba ko zai iya magance taƙaddamar dake cikin jam'iyar ta NDC mai jan ragamar mulki. Tun ba yau ba ake fama da rikici tsakanin marigayi Mills da iyalin gidan tsohon shugaban ƙasa kuma mutumin da ya kafa jam'iyar NDC wato Jerry Rwalings. Ko mutuwar Mills za ta sa a ɗinke wannan ɓaraka? Ga dai ra'ayin Daniela Kuzu ta gidauniyar Friedrich-Ebert a birnin Accra.

Ghana's Vice-President John Dramani Mahama (C) sits after taking the oath of office as head of state, hours after the announcement of the death of Ghana's President John Atta Mills, in the capital Accra, July 24, 2012. Mills, who won international praise for presiding over a stable model democracy in Africa, died suddenly on Tuesday and his vice-president was quickly sworn in to replace him at the helm of the oil, gold and cocoa producer. Mahama, 53, will serve as caretaker president until the elections at the end of the year. REUTERS/Yaw Bibini (GHANA - Tags: POLITICS ELECTIONS TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

"Gaskiya a bayyane ya ke cewa 'yan gidan Rawlings ba su da kyakkyawar dangantaka da Mahama. Kuma hakan ka iya ci-gaba kamar yadda aka saba. Ba wanda zai iya yin hasashen irin matakan da iyalan gidan Rawlings za su ɗauka bayan mutuwar Mills, ko za su nemi wasu haƙoƙinsu."

Mills ya taka rawar gani wajen shiga tsakanin jam'iyun ƙasa

In dai ba a manta ba uwargidan Rwalings wato Nana Konadu Agyeman Rawlings ta sha kaye a hannun Mills a zaɓen fid da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar NDC a zaɓe mai zuwa. Martin Wilde shi ne tsohon daraktan gidauniyar Konrad-Adenauer a Ghana ya yaba wa tsohon shugaban Ghana marigayi John Atta Mills musamman dangane da rawar da ya taka na shiga tsakanin jam'iyun ƙasar.

Titel: NDC (National Democratic Congress) leade... Bildunterschrift: ACCRA, GHANA: NDC (National Democratic Congress) leader and presidential election candidate Pr John Atta Mills (R) talks to former Ghanaian President Jerry Rawlings during a meeting in Accra 04 December 2004. Ghana will hold presidential elections next 07 December. AFP PHOTO ISSOUF SANOGO (Photo credit should read ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images) Erstellt am: 04 Dez 2004 Editorial-Bild-Nummer: 51824067 Beschränkungen: Bei kommerzieller Verwendung sowie für verkaufsfördernde Zwecke kontaktieren Sie bitte Ihr lokales Büro. Vollständige redaktionelle Rechte in Großbritannien, USA, Irland, Italien, Spanien, Kanada (außer Quebec). Eingeschränkte redaktionelle Rechte in allen anderen Ländern. Wenden Sie sich bitte an Ihr lokales Büro. This image is only available in Getty Images offices in the United Kingdom, United States, Germany (Austria, Switzerland via Germany), and Australia. Lizenztyp: Lizenzpflichtig Fotograf: ISSOUF SANOGO/Fest angestellter Fotograf Kollektion: AFP Bildnachweis: AFP/Getty Images Max. Dateigröße/ Abmessungen/ dpi: 9,00 MB - 2109 x 1491 Pixel (17,86 x 12,62 cm) - 300 dpi Die Dateigröße für den Download weicht u. U. von den Angaben ab. Quelle: AFP Releaseangaben: Kein Release verfügbar. Weitere Informationen Strichcode: AFP Objektname: PAR2004120494774 Urheberrecht: 2004 AFP Suchbegriffe: Anführen, Ghana, Reden, Treffen, Politik, Redner, Präsident, Politische Wahl, Präsidentenwahl, Accra, Früherer, Jerry Rawlings, John Atta Mills, Kongressversammlung. Nach ähnlichen Bildern suchen Verfügbarkeit: Die Verfügbarkeit dieses Bildes kann erst beim Kauf garantiert werden.
Jerry Rawlings da marigayi John Atta MillsHoto: Getty Images

"Babban abin yabo ga Mills shi ne gudunmawar da ya bayar wajen wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna a siyasar cikin gida. Ladar da ya samu ita ce ɓaraka a tsakanin jam'iyarsa. Saboda da rashin lafiyarsa ya rasa wani karsashin aiwatar da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a tsakanin manyan jami'an gwamnati."

Babban ƙalubalen da ke gaban shugabannin siyasar Ghana a shekaru masu zuwa shi ne yadda za a yi amfani da arzikin man fetir ɗin ƙasar. Shin talakawa za su gani a ƙasa kamar a ƙasar Botswana ko kuwa arzikin zai kwarara aljihun 'yan siyasa ne kamar a Najeriya?

Mawallafa: Adrian Kriesch / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu