Makomar tallafin soja a Ukraine
July 17, 2024A kasafin kudin da majalisar dokokin Jamus ta amince da shi a wannan Laraba, Jamus a badi za ta rage taimkon soja da take baiwa Ukraine da Euro biliyan hudu, wato kusan rabin agajin da ta ware wa Ukraine a bana. A cewar mahukuntan Jamus suna fatan Ukraine ta iya yin nata kokarin na cimma burin da ake so wajen samar wa sojanta kudin aiki, idan aka baiwa Ukraine bashin dala biliyan 50 da aka amince a dauka cikin kudin Rasha da kasashen Yamma suka rike bayan barkewar yakin Ukraine. Ministan kudin Jamus Christian Lindner yace samarwa Ukraine kudin an kebe shi, godiya ta tabbata bisa alkawarin ksashen EU da kuma kasashen G7 masu karfin tattalin arzikin masana'antu na duniya. Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da cikin shugabannin Turai ya duri ruwa bayan da Donald Trump ya sanar da sunan mataimakinsa wanda ya yi fice wajen adawa da tallafin soja wa Ukraine, kuma mutumin da ke neman sai Turai ta bar dogaro da Amirka fannin tsaro.