Makuddan kudaden sallama ga jami'ai a Kenya
January 12, 2013Shugaban Kenya ya hau kujerar na-ki game da dokar da 'yan majalisar dokokin kasar suka zartar, a lokacin zamansu na karshe, inda suka amince da baiwa kawunansu garabasar kudade gabannin gudanar da zabukan kasar. A wannan Asabar ce shugaba Mwai Kibaki ya baiwa babban mai shari'a na kasar umarnin sake tsara dokar, ta yadda za ta dace da tsarin mulkin kasar.
Kudirin dokar da 'yan majalisar suka yi naa'am da shi a ranar Larabar da ta gabata dai, ya tanadi baiwa kowane dan majalisar dokoki daya kudi dalar Amirka dubu 110, a matsayin kudin sallama. Hakanan a karkashin dokar, kowane dan majalisa zai sami jami'in tsaron lafiyarsa, da fasgo irin na diflomasiyya da kuma matsayi - irin na manyan jami'ai a tashoshin jiragen sama.
Sai dai kuma hukumar kula da harkokin albashi da alawus-alawus ta kasar Kenya ta ce matakin da 'yan majalisar dokokin suka dauka ya sabawa doka - a karkashin tsarin mulkin da kasar ta yi na'am da shi a shekara ta 2010. A dai kasar Kenya matsakaicin ma'akaikaci na karban albashin kimanin kudi dala 1,700 ne a duk shekara.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe