Malesiya na takun saka da Koriya ta Arewa
March 7, 2017Talla
Ma'aikatar cikin gidan kasar Malesiya ce ta bayyana daukar wannan mataki da nufin tantance wasu jami'an da ake zargi da hannu wajen kisan dan uwan shugaban Koriya ta Arewar. To sai dai wannan zazzafar mataki na zuwa ne adai-adai lokacin da rahotanni ke tabbatar da hukuncin da Koriya ta Arewa ta ayyana, na haramta wa 'yan Malesiya mazauna Koriya ta Arewa ficewa da ga kasar a wannan Talata. Wannan dai na zuwa ne a wani batu da ake ganin ya kai kololuwar tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu a kan zargin kashe dan uwan shugaban kasar Koriya ta Arewar.