1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malesiya ta kira jakadanta a Pyongyang

Yusuf Bala Nayaya
February 20, 2017

Ma'aikatar harkokin wajen Malesiya ta ce kiran jakadan ya zama dole duba da halin da aka shiga saboda rasuwar dan uwan shugaban Koriya ta Arewa a kasarta.

https://p.dw.com/p/2Xshp
Mutmaßlich Kim Jong Nam, Bruder von Nordkoreas Diktator Kim Jong Un
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Kambayashi/W. Maye

Kasar Malesiya ta nemi jakadanta ya koma gida daga birnin Pyongyang fadar gwamnatin Koriya ta Arewa, abin da ke zuwa bayan da aka shiga nuna yatsa tsakanin kasashen biyu sakamakon rasuwar daya daga cikin iyalan masu mulki a wannan kasa ta Koriya ta Arewa.

Ma'aikatar harkokin wajen Malesiya a ranar Litinin din nan ta ce ta kira jakadan nata ne, saboda a zauna a tattauna da shi, har ila yau ta kuma kira Jakada Kang Chol na Koriya ta Arewa domin ya yi karin bayani kan zargin da ya yi wa mahukuntan na birnin Kuala Lumpur.

Shi dai Kang  ya ce kasar ta Malesiya na neman yin rufa-rufa kan binciken gawar Kim Jong Nam wanda aka shiga binciken gawarsa a Malesiya ba tare da tuntubar bangaren gwamnatin kasar ta Koriya ta Arewa ba a cewar sa. Kim Jong Nam da ya mutu a Malesiya dai ya kasance dan uwa ga Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

Ma'aikatar harkokin wajen ta Malesiya ta ce bayanan da jakadan na Koriya ta Arewa ya yi ba su da tushe ballantana makama.