Zanga-zanga ta barke a Mali
July 10, 2020Talla
Tun daga farko dai kawancen mai suna M5 ya gindaya wasu muhimman sharudda ga gwamanati da ciki har da rusa majalisar dokoki da kotun tsarin mulki hakan da nada wani sabon firaministan da zai fito daga bangaren 'yan adawa, to amma sai dai a wani mataki na yayyafawa wutar fitinar ruwan sanyi, shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya ambaci sake duba batun sakamakon zaben da kotun tsarin mulkin kasar ta lamunta da shi na 'yan majalisar dokoki, wanda masu nazari ke yiwa kallon shine musabbabin born da zanga-zangar.
Wannan dai shi ne karo na uku kenan a kasa ga watanni biyu da al'ummar Malin ke fitowa yin zanga-zangar kin jinin gwamnatin a kasar da ke fama da hare-haren kungiyoyin jihadi da fadace-fadacen kabilanci.