1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar samar da gwamnatin hadaka

Binta Aliyu Zurmi
July 19, 2020

Masu shiga tsakani a rikicin kasar Mali daga kasashen yammacin Afirka, na kira da a kafa gwamnatin hadin kan kasa da kuma samar da sabbin alkalai a kotun kundin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/3fZN6
Ibrahim Boubacar Keita
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Bayan kwashe kwanaki ana tattaunawa tsakanin gwamnati da ma bangaren 'yan adawa, masu shiga tsakanin daga kasashe 15 na kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, sun bada shawarar samar da gwamnatin hadakar da za ta dauki kaso hamsin, kaso 30 kuma ya zo daga bangaren 'yan adawa kana kaso 20 ya zo daga kungiyoyin jama'a.

Zarge-zargen cin hanci da rashawa da nuna halin ko in kula a rigingimun da suka lakume dubban rayuka na daga cikin batutuwan da suka harzuka jama'a wajen tilasta wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keita yin murabus bayan shafe sama da shekaru takwas ya na mulki.