1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso da Mali da Nijar sun caccaki matakan ECOWAS

Abdoulaye Mamane Amadou
December 31, 2023

Firaministocin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, sun sha alwashin inganta hulda da inganta makomar al'ummomin kasashensu, duk da matsin daga kungiyar ECOWAS

https://p.dw.com/p/4ajkK
 Shugaban kasar Mali Assimi Goïta I Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani I Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traoré
Shugaban kasar Mali Assimi Goïta I Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani I Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traoré Hoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun bayyana anniyarsu ta karfafa hulda da samar wa al'ummominsu makoma mai kyau, a karkashin inuwar kawancen da suka kulla na Alliance des Etats du Sahel (AES).

Karin Bayani   Sabon kawancen tsaro na Sahel zai fuskanci kalubale

A yayin wani taron hadin gwiwa da suka gudanar a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, Firaministocin Burkina Faso da Mali da Nijar, sun ce nan ba da jimawa ba kasashen za su gabatar da wasu muhimman tsare-tsare, ciki har da na shimfida layin dogo a tsakaninsu, da gine-ginen hanyoyi a karkashin wani kwamitin tuntubar da za su kafa na hadin gwiwa.

Kasashen sun kuma yi kakkausar suka game da takunkuman karayar tattalin arziki da kungiyar Ecowas ta kakaba musu, tun bayan kifar da gwamnatocin dimukuradiyya.

Karin Bayani  ECOWAS na kan bakanta a kan Nijar

Nan gaba a yau ake dakon firaministocin biyu da mai masukinsu na Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine, su halarci birnin Agadez domin kawo karshen gasar cin takobin shekara-shekara na kokawar gargajiya, wasa mafi tasiri da daukar hankali a Nijar.