1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manchester: An kara tsaro bayan harin mai alaka da IS

Aliyu Muhammad Waziri
May 24, 2017

Mahukunta a Birtaniya sun ce matashin dan kunar bakin waken nan da ya halaka rayuka a birnin Manchester cikin daren Litinin ya ziyarci Siriya baya ga ziyarar Libiya da ya yi a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/2dSBo
Großbritannien Manchester Gedenken
Hoto: DW/L. Bevanger

Ministar harkokin cikin Birtaniya Amber Rudd ta bayyana haka ne bayan kalaman Firaministar kasar da ke nunin girman barazanar ta’addanci da ke a kasar.

Ministar cikin gidan Birtaniya Amber Rudd da takwaranta na kasar Faransa sun fada cewar dan kunar bakin waken Salman Abedi ya kitsa wannan harin, hari ne tare da taimakon wasu masu wannan akida ta ta’addanci, kuma ba su da wata shakkar alakarsu da kungiyar nan ta IS.

Gwamnatin Birtaniyar ta ce a bayyane take cewar kasar na cikin tsananin matsayi na iya fuskantar wasu hare-hare, a saboda hakan ne aka tsaurara tsaro a muhimman wurare a fadin kasar, inda tuni ma aka wadata wuraren da sojoji saboda matakan ko ta kwana.

UK | England erhöht Terrorwarnstufe
Hoto: Reuters/S. Wermuth

Jami’an ‘yan sandan kasar ma dai sun tabbatar da nasarar kama wasu mutane uku a Kudancin birnin na Manchester a wannan Laraba, da kuma suka yi amannar suna da hannu a harin da ya halaka rayuka, sai dai ba su yi wani karin bayani ba.

Rahotanni sun tabbatar da ganin dakaru dubu uku da 800 da aka girke a muhimman tituna, misali fadar Buckingham da Downing Street, matakin da ke baiwa jami’an ‘yan sanda damar mayar da hankali ga sintiri gami da bincike.

 A birnin London ga an sami karuwar dakaru 984, da mahukuntan birnin suka bukata tun farko.   

Ministar cikin gidan birtaniya Amber Rudd, ta kara da cewa:

“Yanzu dai za a ga sojoji 3,800. Mun kuma yi hakan ne bayan tattaunawa da manyan jami’an ‘yan sanda da sauran al’uma, sai kuma na ba da umurni. Wadannan matakan dai a jiya ne muka tsara su. Za kuma mu ci gaba a hakan na lokaci mai tsawo. Mun samar da isassun kudade don tabbatar da nasarar aikin. Mun kuma baiwa suma jami’an ‘yan sanda goyon bayan da suke bukata kuma za mu kafu a kan haka.

UK | Trauerbekundungen nach dem Anschlag in Manchester
Hoto: picture-alliance/empics/B. Birchall

Sai dai a halin da ake ciki, mahukuntan na Birtaniya, sun bayyana bacin rai kan wani azarbabin da jami’an Amirka suka yi, na bayar da wasu bayanai muhimmai masu alaka da harin, bayanan da jami’an Birtaniya ke cewa ba su shirya sanar da su ba.

Shi dai maharin Salman Abedi, wanda haifaffen kasar Birtaniya ne

Ya tarwatsa kansa ne a cibiyar raye raye ta Manchester Arena inda dubban matasa da kuma kananan yara suka halarta don shaida wasan da wata mawakiya daga Amirka Ariana Grande ta yi.

Harin ya halaka mutane 22 ciki har da wata ‘yar shekara takwas da ma wasu yaran, yayin da sabbin alkaluma ke cewa mutane 64 ne suka jikkata.