Maniyyata sun fara gudanar da aikin Hajjin bana
June 26, 2023Ana sa ran fiye da mutane miliyan biyu da dubu dari biyar daga kasashe 160 na duniya ne za su sauke farali a kasa mai tsarki a wannan shekarar.
Hukumar kula da aikin Hajji da Umra ta Saudiya ta ce idan har komai ya tafi yadda aka tsara, a bana za a gudanar da aikin Hajji mafi yawan al'umma cikin tarihi.
Hakan dai zai samu ne sakamakon wannan shi ne karon farko da za a gudanar da aiki hajji tun bayan shekarar 2019 ba tare da dokokin corona ba.
A daren jiya Lahadi ne dai, maniyatan suka fara tafiya wuraren ibada da suka hada da Mina daga masallacin Harami gabanin ranar hawan Arfa a gobe Talata.
Hukumomi sun ce an tanadar da abinci da kuma karin jami'an tsaro a Mina, birnin mafi yawan tantuna a duniya. Aikin hajji na daga cikin shika-shikan musulumci guda biyar, da ya wajaba a kan ko wane Musulmi a kalla sau daya a rayuwarsa idan yana da iko.