Manufar harin Izraela a kan makaman Siriya
November 1, 2013Rahotanni daga yankin gabas ta tsakiya na nuni da cewar, Sojojin Izraela sun kai hari ta sararin samaniya a kan wasu kayayyakin sojin Siriya. Harin na Izraela dai acewarta, na da nufin dakatar da kai wa 'yan Hizbolla na kasar Lebanon makamai. Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da masu binciken suka sanar da cewar, sun cimma killace dukkan makamai masu guba da ke Siriya. Gidan talabijin na Al-Arabiyya ta gwamnatin Saudi Arabiya ta ruwaito cewar, harin jiragen yakin Izraela ya ritsa da sansanin kayayyakin soji na Siriya da ke gunduwar Latakia, wanda acewarsu ake shirin kai wa kungiyar ta 'yan Shi'a da ke Lebanon. A watan Mayu ne dai Izraelan ta kai hare hare sau biyu a cikin Siriya ta sararin samaniya, kuma a wancan lokacin wani babban jami'in Izrelan ya sanar da cewar, hare haren na da nasaba da tsayar da makaman Iran da ake shirin kai wa 'yan Hizbolla. Jami'an kungiyar hana yaduwar makamai masu guba dai, sun tabbatar da cewar sun rufe dukkan wuraren ajiyar makamai masu guba da ke Siriya.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu