1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofin Bankin Duniya wajen rage talauci a Afrika

Zainab A MohammadJune 8, 2005

Ziyarar sabon shugaban bankin duniya Paul Wolfowitz a kasashe hudu na Afrika a mako mai zuwa

https://p.dw.com/p/BwUS
Hoto: AP

Bankin duniya zai inganta tallfinsa wa Nahiyar Afrika,domin rage radadin talauci da wasu kasashen nahiyar ke fama dashi,ta hanyar inganta tattalinsu kwatankwacin na kasashe dake da cigaban tattali.

Domin tabbatar da wannan yunkuri ne,sabon shugaban Bankin duniya Paul Wolfowitz zai kai ziyara kasashe 4 a nahiyar ta Afrika a mako mai gabatowa.

Shugaban Bankin wanda ke kasancewa tsohon mataimakin ministan tsaro na Amurka ,zai kai ziyara zuwa manyan kasashen Afrika biyu kuma zakaru dake jan akalar Nahiyar watau Nigeria da Afrika ta kudu ,ayayinda kuma zai yada zango a Rwanda da Burkino Faso.

Shugaban bankin wanda ya haye karagar mulki ranar 1 ga watan yuni ya bayyana cewa,Bankin duniya da wasu hukumomi na raya kasashe zasu sake mayar da hankalinsu kan nahiyar Afrika da kyakkyawan fata na alheri,na tsame ta daka kangin da a yanzu haka take ciki.

Mr Wolfowitz yace bawai wannan ziyara tasa daya ce zata maganta wadannan matsaloli da alumman wadannan kasashe ke fuskanta ba,amma yayi alkawarin cigaba da komawa lokuta daban daban a shekaru masu gabatowa ,domin wannan shine somin tabi.

Yace yayi imanin cewa shugabannin Afrika na Magana da muryoyi daban daban kana da sabanin raayi kan muhimman batutuwa da suka hadar da rashawa a wannan nahiya,idan aka kwatanta da shekaru 10 a baya,wanda hakan ya zamanto kalubale da kuma daman a taimakawa nahiyar.

Mr Gobind Nankani dake zama mataimakin Bankin duniya ta shiyyar Afrika ya fadawa kamfanin dillancin labaru na reuters cewa,manufofin Wolfowitz zasu bukaci yiwa kasashen Afrika gyaran fuska,ta yadda matalauta da masu arzikin nahiyar zasuci gajiyarsu.

Da tallafin ayyauk guda 334 da kimanin kudi dalan Amurka billion 16.6,bankin duniya na mai kasancewa mai bada tallafi mafi tsoka wajen raya kasashen Afrika.

A dangane da hakane Mr Nankani ya jaddada bukatar goyon bayan kasashe ta fanning daukan matakai da suka dace wajen yakan talauci,da inganta cigaba.Wannan yunkuri na tallafawa Afrika daga bankin duniya yazo adaidai lokacinda kasashe masu cigaban masanaantu a duniya ke kokarin cimma daidaito wajen rage basussuka da talauci dake addaban nahiyar.

A wata ganawa da yayi jiya da shugaba George w Bush na Amurka a Washinton jiya,prime ministan Britania Tony Blair ya gabatar da shirinsa na Karin tallafin raya kasashen Afrika tare da yafe basussuka da kasarsa ke binsu.

Mr Nankani na bankin duniya ya lura dacewa irin rawa da bankin duniya ke takawa a tsakanin kasashen Afrika ,ya taimaka matuka gaya wajen inganta harkokinsu na kasuwanci.

Bisa ga wannan ne yace bankin zata bada Karin rance wajen gudanar da ayyukan inganta cigaba da suka hadar da gyaran hanya,da inganta samara da ruwan sha mai kyau,da muhalli mai tsabta da wutan lantarki,fiye daga dala billion 1.8 da take bayarwa a shekara izuwa dala billion 3.

To sai dai yace wannan shine mataki na farko na wannan tallafi,domin nahiyar na bukatar agajin dala billion 17 a shekara,idan har ana son ta samu ingantuwa zuwa kashi 7 daga cikin 100,a shekara.wanda hakan ne kadai zai yaki talauci.

Mr Nankani yace yanzu haka nahiyar Afrika na rabe kashi biyu tsakanin kawashen dake da nasara cikin harkokin tattalin arikinsu da suka hadar da Ghana da Senegal da Mozambique da Burkino faso, kana a hannu guda kuma wadanda ke cigaba da kasancewa cikin kangin talau wadanda sune sukafi rinjaye.

Ya kara dacewa manyan kasashe kamar Nigeroa da janhuriyar democradiyyar Congo da Sudan da Ethiopia sun nuna kwazonsu ne kadai bayan lokaci mai tsawo na rashin zaman lafiya da matsaloli na tattali.