Manyan 'yan takara a zaben Jamus
Zaben majalisar dokoki ta Bundestag na karatowa, su kuma manyan 'yan takarar jam'iyyu suna kokarin nuna kyakkkyawan halayensu. Sai dai bayan halayensu da aka sani a hukumance, akwai kuma na boye.
Wa zai zama shugaban gwamnati?
Duk da cewa jam'iyyun CDU da SPD sun yi amannar cewa daga cikinsu za a samu shugaban gwamnati bayan zaben 'yan majalisar Bundestag a watan Satumba, dukkan manyan jam'iyyun siyasa a Jamus na da manyan 'yan takara. Suna wakiltar jam'iyyunsu a yakin neman zabe. DW na gabatar da su ba kwai yadda aka sansu a hukumance ba, a'a har da rayuwarsu a gida.
A kan kololuwar iko
Tun shekaru takwas da suka wuce Angela Merkel (59) ke jan ragamar mulki a tarayyar Jamus. A 1989 ta fara taka rawa a fagen siyasa a cikin daya daga jam'iyyun Demokradiyya a gabacin kasar sannan ta shiga CDU mai ra'ayin mazan jiya. A matsayin shugabar gwamnati tana kare matsayin jam'iyyarta: Ta yi bankwana da yi wa kasa hidima sannan ta yanke shawara game da rufe tashoshin makashin nukiliya.
Balaguro, girki, shugabanci
Idan tana da lokaci mace mai kamar maza a duniya tana balaguro cikin daji. Tana kaunar yin balaguro da mijinta da kuma girki. Angela Merkel ta girma ne a Jamus ta Gabas. A can ta yi karatun jami'a a fannin ilimin Physics. "Ilimin kimiyar halittu ya kasance abin da nake so, domin wani abu ne da shugabannin Jamus ta Gabas ba su yi wa katsalanda ba", inji Merkel a shafinta na intanet.
Dan takara mai karfi...
Dan takarar SPD, Peer Steinbrück (66), "Ba zai taba" sake yin mulki da Angela Merkel ba. Daga 2005 zuwa 2009 ya kasance ministan kudi karkashin Merkel a cikin babbar gwamnatin kawance ta SPD da CDU. A yakin neman zabe masanin tattalin arziki ya yi kira da kafa dokar da tanadi albashi mafi kankanta da dakile hauhwar kudin haya - inda yake amfani da kalamai na tsokana.
...da daidaita alkibla
Tun yana da shekaru shida Peer Steinbrück yake wasan chess. Idan ba ya karawa da zakaran duniya to sai ya fuskanci na'urar chess. Dan takarar neman shugaban gwamnatin Jamus karkashin SPD ya taba kwatanta wasan chess da wani wasa da a kullum mutum ke kokarin nuna kwarewa a kan abokin karawarsa. "Tun da na fara karawa da komfutar chess, na ga ba ta da wani amfani."
'Yan takara biyu mabanbanta
Kamata ya yi kowa ya ji cewa 'yan takara biyu na jam'iyyar The Greens na wakiltarsa: Katrin Göring-Eckardt (47) ta fi kusanci da jama'a, Jürgen Trittin (59) ya fito daga bangaren 'yan neman sauyi na jam'iyyar. Ta fito daga gabaci shi kuma daga yammacin Jamus. Dukkansu biyu na bukatar a kara haraji ga masu alabashi mai tsoka, jam'iyyar ta tsayar da dukkansu biyu. Wannan shi ne na farko a Jamus.
Kullum ana ciki
Wanka a cikin kogi ba zai canja wa dan takarar The Greens Jürgen Trittin wani abu mai yawa ba. Tsohon minitsan kare muhalli na Jamus ya saba da wuraren da ake zanga-zanga. Domin Trittin ya fi son ana ganinshi a wuraren zanga-zangar neman karin matakan kare muhalli da yaki da wariyar launin fata. Sai dai masanin kimiyar zamantakewa ba ya son yin bayani game da rayuwarsa a gida.
'Yar rawa ta Greens
A gun mahaifinta wanda ke da makarantar koyan rawa a Jamus ta Gabas, Katrin Göring-Eckhardt, ta koyi tafiya a kan kwalaye. Ta ma koyi shiga takarar rawa. Tun sannan ba ta tsoron bayyana gaban taron jama'a. Wani babban sharadi ga tsayawarta takara, shi ne mahaiffiyar yara maza biyu, ta jingine aikinta a matsayin shugabar taron mabiya darikar Evangelika a Jamus.
Tattalin arziki, kudi, Brüderle
Rainer Brüderle (68), dan takarar FDP, dan tattalin arziki. Tun farkon aikinsa a fagen siyasa a Mainz har zuwa mukamin ministan tattalin arzikin Jamus karkashin Angela Merkel, batutuwan tattali arziki ke kan gaban aikinsa. Bayan da FDP ta rasa kuri'u da yawa a matakin jihohi, a shekarar 2011 Brüderle ya yi murabus daga dukkan mukamansa, ya karbi ragamar shugaban jam'iyya a majalisar Bundestag.
Babu rufa-rufa...
A tsakiyar watan Yuni Rainer Brüderle ya karye a kafa da hannu bayan wata faduwa. Ya kammala jinyar tsawon makonni a tafkin Tegernsee. Dan shekaru 68 ya yi korafi yadda neman maganin ya dade lokacin yakin neman zabe. Dan siyasa mai jini a jika, wanda bai ya son bayyana abin da ke faruwa a rayuwarsa ta gida, in ban da yana da aure, dan Evangelika ne kuma a Mainz yake da zama.
'Yan gurguzu da masu tsananin ra'ayin gurguzu
Mataimakiyar shugaban Jami'iyya Sahra Wagenknecht (44) da shugaban bangaren a majalisa Gregor Gysi (65) ba sa kaunar juna sosai kuma ba sa son yin aiki tare. Amma duk da haka suna jagorantar tawagar shugabannin jam'iyar Die Linke a yakin neman zaben shiga Bundestag. Don kada a samu sabani, suna samun taimako daga wasu 'yan takara su shida.
'Yan gurguzu a rayuwar gida
Za a iya cewa ita kadai ce amma a rayuwar gida tana tare da Oskar Lafontaine, tsohon shugaban masu ra'ayin gurguzu na Linke. "Ina bukatar lokacin walwala, lokacin karance-karance da tunani", inji Sahra Wagenknecht lokacin da take bayani game da kanta. Tana da sha'awar yin nazari mai zurfi da bincike cikin batutuwa: Mai rike da digirin digirgir a fannin siyasa, da farko ta son zama 'yar kimiya.
Mai fasaha a magana
Lokacin da yake yaro Gregor Gysi ya yi ta kwaikwayon 'yan wasan drama na Sobiet. Abokansa na sowa ida suka ga sunansa a jerin masu wasa. Yau dai ya fi sha'awar magana game da wasan kwaikwayo, yana karanta makala da sauraon wakokin classic. A da masanin shari'ar na karatun failoli har cikin dare kamar wani mai iskoki. Amma yanzu ko oho domin Gysi yana fama da matsalolin ciwon zuciya.