1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan bayyana rahoton binciken NNPC

Ubale Musa/ Zainab Mohammed AbubakarApril 28, 2015

Muhawara ta barke a Najeriya a tsakanin masu ganin shugaban da ke shirin barin gado ya yi ta maza da kuma masu tunanin ya kwabsa na gabatar da rahota.

https://p.dw.com/p/1FGPS
Nigeria Präsident Goodluck Ebele Jonathan
Hoto: imago/Wolf P. Prange

Babu dai zato ba kuma tsamanni fadar gwamnatin kasar ta Aso rock ta umarci fitar da rahoton da ake yi wa kallo raba gardama a cikin masana'antar man fetur din da ke tsakiyar takaddamar cin hanci yanzu haka.

Akalla dala Milayan dubu 20 ne dai ake fadin an sace a cikin masana'antar da ke zaman tsoka da jini ta 'yan kasar da kuma daga dukkan alamu ta koma mallaki na kalilan.

Kafin rahoton da a cikinsa wani kamfanin binciken kudin kasa da kasa ya ce Eh lallai da akwai almundaha a cikin masana'antar amman kuma su basu hango yawan kudin da ake fadin an lashe ba.

Rahoton kuma da gwamnatin kasar da ke barin gado ke fatan zai wanke ta cikin zargin wadaka da dukiya ta 'yan kasar da ke zaman tagomashi a gareta.

To sai dai kuma fitar da rahoton cikin kasa da wata guda da barin mulki dai na neman jawo kace-nace cikin kasar da ke ganin dama biyu da gwamnatin da ke neman hanyar tsira daga hannun 'yan sauyin cikin kasar ta Najeriya.

Nigeria Selbstmordanschlag 28.07.2014
Hoto: Reuters

Dr Kole Shettima dai na zaman shugaban cibiyar demokaradiya da ci gaba da hedikwatarta ke a Abuja kuma a tunanisa Jonathan ya yi fargar jaji wajen sakin rahoton da ya zo 'yan awoyi bayan da shi kansa shugaban da ke shirin hawa gadon ya ce sai yabi kwakwaf.

To sai dai kuma a fadar kakaki na shugaban da ke barin gadon yanke hukuncin sakin rahoton yanzu bashi da ruwa balle tsaki da tsoro na bincike a zukata na shugaban da ke adabo da kasar.

kokari na ilimantar da 'yan kasa ko kuma kokari na kaucewa rikici, a baya dai gwamnatin kasar ta sha hawa tana danne rahotanni daban daban da suka shafi batun cin hanci dama na tattalin arziki sannan da tsaro.