Wasu limaman Coci sun goyi bayan auren jinsi
May 12, 2021A Jamus, Limaman Cocin Katolika sama da dari ne suka amince tare da bayar da goyan bayansu ga masu mu'amala ko auren jinsi daya. Batun dai, ya dauki hankulan duniya inda wasu ke yabawa da matakin, wasu kuwa na ganin ya sabawa ka'idar darikar Cocin Katolika. Kawo yanzu dai, mujami'u Jamus ba su aminta da hakan a hukumance ba, hakazalika fadar Vatikan ta haramta auren jinsi.
A daya bangaren kuwa, Ministan harkokin wajen Jamus, Heiko Maas zai gana yau, da Fafaroma Francis a fadar Vatikan, ganawar da za su ta sirri, za ta mayar da hankali kan batun cin zarafin yara kanana ta hanyar lalata da ake zargi yayi kamari a tsakanin mayan limaman Cocin.
Maas bayan isa birnin Rome, ya sheda ma manema labarai cewa, ya damu kwarai da wannan batu zai kuma so ya ji, matakin da Fafaroman ke shirin dauka kan matsalar. Ministan na Jamus, shi ne na farko da ke irin wannan ganawa da shugaban Cocin Katolikan a tsawon shekaru ashirin da suka gabata.