1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan magoya bayan IS a Pilipin

Yusuf Bala Nayaya
May 30, 2017

Fiye da mutane 100 ne aka tabbatar da rasuwarsu tun bayan da fada ya barke a ranar Talatar makon jiya, inda mayaka dauke da tutar IS suka mamaye birnin Marawi, abin da ya sanya sojojin kasar mayar da martani.

https://p.dw.com/p/2dnqa
Unruhen Philippinen Militär IS Marawi
Hoto: Getty Images/T.Aljibe

Mahukuntan Pilipin sun ce mayakan da suka mamaye fararen hula a birni  Marawi da ke kudancin kasar da sunan kishin Islama, na da damar mika wuya. Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da dakarun sojan gwamnati ke amfani da jirage masu saukar ungulu wajen harba makaman roka a yankin da masu tada kayar bayan suka ja daga. Fiye da mutane 100 ne dai aka tabbatar da rasuwarsu tun bayan da fadan ya barke a ranar Talatar makonda ya gabata, inda mayakan dauke da tutar IS suka mamaye birnin na Marawi da ke da rinjaye na mabiya addinin Islama.

Tuni dai Shugaba Rodrigo Duterte ya bada umarni ga sojoji da su karbi harkokin gudanarwar yankin Mindanao da ke da al'umma kimanin miliyan 20, a matsayin wani mataki na mayar da martani kan yadda mayakan sa-kai a yankin ke nuna goyon bayansu ga kungiyar IS, abin da ya sa ya ce sun zama babbar barazana.