1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan makamai masu guba a Siriya

September 17, 2013

Kasashen duniya sun fara mayar da martani mabanbanta dangane da rahoton da masu binciken makamai na Majalisar Dinkin Duniya a Siriya suka gabatar a ranar Litinin.

https://p.dw.com/p/19iZn
Hoto: Reuters

Kunshin rahoton dai ya tabbatar da cewar bisa ga binciken da aka gudanar an gano cewar makaman da aka yi amfani da su sun kunshi sinadarin na Sarin mai kashe laka, sai dai masu bincinke ba su fayyace wanda ya yi amfani da makaman ba tsakani gwamnatin Bashar al-Assad da bangaren da ke adawa da shi.

Kasashe irin su Burtaniya da Faransa dai sun yanke shawarar cewar Assad ne ke da hannu wajen amfani da makaman don a cewarsu 'yan tawayen kasar basu da karfin da za su iya samunsu yayin da wasu kasashen ciki har da Rasha wadda ke dasawa da Assad din ke cewar gwamnatin kasa ba ta hannu.

Tuni dai sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a wani jawabi da ya yi a jiya ya ce kunshin rahoton na da tada hankali kuma abinda aka gano dangane da amfani da makaman masu guba daidai yake da aikata laifukan yaki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe