1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun binciken hare-hare a Jihar Borno ta Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB
August 22, 2018

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi nemi hanzarta hukunta mutanen da ke da hannu a harin da ya yi dalilin mutuwar mutane 19 a garin Mailari na Jihar Borno da ke Najeriya lamarin da ya sanya mayar da murtani.

https://p.dw.com/p/33Zt9
Maiduguri Nigeria Boko Haram Anschlag
Hoto: Reuters/A. Kingimi

Karuwar kai munanan hare-hare da ake dangata su da kungiyar Jama'atu Ahlu Sunnah Li Dawatti Waljihad da ake kira Boko Haram ya sanya Majalisar Dinkin Duniyar ta bakin sakatarenta Antonio Guterres bayyana damuwarsa tare da yin Allah wadai da yawaitar zubar da jinni, tare da kiran a hanzarta tabbatar da yin adalci. Kara tabarbarewar yanayin tsaron da ya sanya shugaban Najeriya bai wa jami'an tsaro umurni su kara kaimi.

Nigeria Maiduguri Airport Ambulanz Leichentransport UN Anghörige
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Najeriya tana kokari na kare kanta cewa tana iyakar kokarinta, to sai dai batu na kamanta adalci a daukacin al'amari na zama muhimmi, musamman ga mutanen da aka kashe musu ‘yan uwansu, abin da ya sanya Majalisar Dinkin Duniyar bukatar ganin an hanzarta yin hakan.

Gaza daukan mataki na dakile karuwar kai hare-hare a lokacin damuna na jefa damuwa da ma tambayar shin mai ke hana jami'an tsaron Najeriya koyon darashi a shekaru tara da Najeriya ta yi tana fama da matsalar ta'adanci? A yayin da ake fama da wannan Majalisar Dinkin Duniyar tana bayyana fuskantar gibi a kudadden da take bukata na aikin jinkai a jihohin Borno, Adamawa da Yobe a kokari na kai dauki ga mutane sama da milyan shida da ke yankin.