Martani kan neman kudin yaki da Boko Haram
July 18, 2014Kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin dan Adam da sauran ‘yan Najeriya sun bukaci ‘yan majalisar dokokin ta Tarayyar Najeriya da su yi watsi da bukatar da Shugaban Jonathan ya gabatar na karbo bashin dalar Amurka biliyan daya domin karfafa yakin da kasar ke yi da kungiyar Boko Haram.
Tun bayan da shugaban ya aike da wannan sako na neman majalisar dokokin kasar ta amince masa karbo bashi na domin kara kaimi da sayan kayan aiki na amfanin jami'an tsaron kasar, a kokarin da suke na murkushe aiyukan ‘yan kungiyar Boko Haram. Tuni kungiyoyin fararen hula suka fara nuna rashin gamsuwa da matakin.
Kungiyoyin sun bayyana cewa daga shekara ta 2010 zuwa 2013 an ware sama da Naira tiriliyon uku da sunan aiyukan tsaro kuma ya zuwa yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
A wata sabuwa kuma wannan bukata ta Shugaba Jonathan ta samu tsaiko bayan da majalisar dokokin ta fara hutu na watanni biyu, abin da ke nufin cewa za a dauki lokaci mai tsawo kafin ta yi muhawara kan wannan batun tare da amincewa da bukatar bashin domin yaki da Boko Haram.
Mawallafi: Amin Suleiman Mohammad (daga Gombe)
Edita: Suleiman Babayo