1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan sabuwar gwamnatin Kwango

Ahmed Salisu GAT
August 27, 2019

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, Shugaban kasar Felix Tshisekedi ya girka gwamnati mai mambobi 66 a karkashin jagorancin Firaminista Sylvestre Ilunga.

https://p.dw.com/p/3OZ5L
Kongo | Präsident Felix Tshisekedi und Premierminister Sylvestre Ilunga Ilunkamba
Shugaba Felix Tshisekedi na Kwango Kinshasa da Firaministansa Sylvestre IlungaHoto: Presidence RDC/G. Kusema

Bayan shafe watanni takwas kan gadon mulki biyo bayan zaben da ya ba shi nasara, shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango Felix Tshisekedi ya girka gwamnati a jiya Litinin. Sai dai masu sanya idanu kan lamuran siyasa a kasar da ma kungiyoyin farar hula sun fara nuna rashin amincewarsu da wasu daga cikin wadanda aka nada saboda abin da suka kira rashin kwarewa da kuma irin alakar da wasu daga cikin ministocin ke da ita da tsohon shugaban kasar Joseph Kabila 

Al'ummar Jamhuriyar Demukuradiyyar Kwango dai ta jima tana dakon ganin an girka gwamnati a kasar. Kuma wannan jira ya kare bayan da a ranar Litinin 26 ga atan Agustan nan aka fidda sunan firaminista da kuma ministocin da za su yi aiki da shi watanni takwas bayan da Shugaba Tshisekedi ya karbi ragamar jagorancin kasar. Jam'iyyun da suka yi kawance a lokacin zabe da kuma 'yan siyasa da ke da karfin iko a kasar dai sun yi ta kai-ruwa-rana kafin a kai ga fidda sunayen ministocin inda daga bisani aka bayyana cewar gwamnatin Kwango za ta kunshi ministoci 66.

Kongo | Premierministers Sylvestre Ilunga Ilunkamba in Kinshasa
Firaministan Kwango Kinshasa Sylvestre Ilunga da makarrabansaHoto: Presidence RDC/G. Kusema

Bisa ga alkaluman da aka fidda dai jam'iyyar FCC ta tsohon shugaban kasar wadda dama ita ce ke da rinjaye a majalisun dokokin kasar ta samu ministoci 42 yayin da kawance jam'iyyun da shugaban kasar na yanzu ke jagoranta ke da ministoci 24. Tuni dai al'ummar kasar ta fara bayyana ra'ayoyinta kan gwamnatin da aka nada inda wasu ke kokawa kan karancin mata da aka samu don a cikin ministocin 66, 13 ne kawai mata. Su kuwa kungiyoyin fararen hula a nasu bangaren nuna rashin gamsuwarsu suka yi da wasu daga cikin ministocin da aka nada. Jeane Claude Katende dan rajin kare hakkin dan Adam ne a kasar:


"An sanya mutanen da a baya suka rike mukami na gwamnati sannan ba su cika irin sharrudan da aka gindaya kafin su shiga gwamnati ba. Mu 'yan kungiyoyin fararen hula na Kwango na kira ga gwamnati da ta mutunta kundin tsarin mulki yayin gudanar da aikinta sannan ta yi aiki wajen ganin ta ciyar da al'umma gaba".

To sai dai duk da nuna rashin amincewar da 'yan fararen hular suka nuna saboda sanya wasu daga cikin na hannun daman Kabila da a baya suka rike mukami, wani bangare na al'ummar kasar na Allah san barka don kuwa a cewarsu sun yi mutanen da suka saba rike mukamai za a maido da su amma kuma sai gashi an sami sabbin fuskoki.

A daura da martanin da 'yan kasar ke mayarwa kan sabuwar gwamnatin ta Kwango, su kuwa abokan arzikin kasar ciki kuwa har da gidauniyar nan ta Konrad Adenauer da ke aikinta a birnin Kinshasa, cewa ta yi fitar jerin sunayen sabbin ministocin ya bude wani sabon babi na dangantaka kyakkyawa tsakanin kasar da sauran kasashen duniya musamman ma da yake galibin wadanda aka nada ba su da matsala tsakaninsu da wata kasa ciki kuwa har da Kungiyar EU kamar yadda Benno Müchler babban daraktan gidauniyar a Kinshasa ya shaida wa DW:

Sylvestre Ilunga Ilunkamba des. Premierminister DR Kongo
Firaministan Kwango Kinshasa Sylvestre IlungaHoto: Presidence RDC


"A cikin wadandan aka nada ministocin babu wanda Kungiyar EU ta sanya wa takunkumi kuma yayin wata ziyara da ya kai kasar a baya-bayan nan ministan raya kasashe na Jamus Gerd Müller ya ce Jamus za ta ci gaba da hulda da Kwango da zarar ta girka gwamnati, huldar da mahukuntan Berlin suka katse ta a shekarar 2017 bayan da Shugaba Kabila ya ci gaba da kasancewa kan gadon mulki duk kuwa da cewar wa'adin mulkinsa ya kare"

Yanzu haka dai al'ummar kasar ma mazauna kasashen ketare na zuba idanu don ganin kamun ludayin gwamnati da kuma irin yunkurin da za su yi wajen daidaita lamura a kasar wadda da dama ke cewar rashin kyakkyawan shugabanci ya durkusar da ita.