1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan salon mulkin Trump

Mouhamadou Awal Balarabe
January 30, 2017

Shugaba Donald Trump na Amirka na ta shan suka daga ko ina cikin duniya kan matakin da ya dauka na haramta wa 'ya'yan wasu kasashe bakwai da Musulmi ke da rinjaye, shiga kasar da yake mulka.

https://p.dw.com/p/2Wfwe
Sabon shugaban kasar Amirka Donald Trump
Sabon shugaban kasar Amirka Donald TrumpHoto: picture-alliance/Olivier Douliery/CNP/AdMedia

Tuni dai wasu gwamnatoci ciki har da Iran suka fara daukar matakai don rama wa kura aniyarta, a inda ta yanke shawarar haramta wa Amirkawa shiga kasar, bayaga zanga-zanga da tofin Allah tsine da kuma matsin lamba da ke ci gaba da gudana a sassa daban-daban na duniya domin tilasta wa shugaban Amirka lashe amansa dangane da rufe kofofin kasarsa da yayi ga wasu kasashe bakwai. A yanzu haka dai fiye da 'yan Birtaniya miliyan daya sun sa hannu a kan wata takarda domin tilasta wa gwamnatinsu soke ziyarar da Donald Trump zai kai kasar.

Matakin ba ya da alaka da addini

 

Zanga-zangar goyon baya da tayin lauyoyi na tsaya wa wadanda aka hana shiga Amirka a filin jirgi
Zanga-zangar goyon baya da tayin lauyoyi na tsaya wa wadanda aka hana shiga Amirka a filin jirgiHoto: DW/M. Shwayder

Sai dai cikin wata sanarwa da ya fitar, Trump ya ce wannan mataki na shi ba shi da dangantaka da addini amma ya daukeshi ne bisa dalilai na tsaro musamman yaki da ayyukan ta'addanci. Tuni ita ma Iraki da ke zama daya daga cikin kasashen da matakin ya shafa ta rama wa kura aniyarta, inda 'yan majalisunta suka kada kuri'ar amince wa da dokar da zata haramta wa Amirkawa shiga kasarsu. Lamarin da zai kawo tsaiko a dangantakar kasashen biyu musamman ma a fannin yaki da ayyukan ta'addanci da kuma cinikayya. Su kuwa 'yan gudun hijirar Siriya da ke Lebanon sun nuna fargaba sakamakon yaduwa da wannan mataki zai iya yi. Dai-dai da masu fada a ji na kasar Amirka ba a barsu a baya ba wajen sukar shugaban kasar tasu, inda baya ga 'yan adawa na jam'iyyar Democrat su ma 'yan Republican suka bi sahu. Shugabannin kanfanoni da dama sun yi tayin bada masauki da ma aikin yi ga Musulmi da aka haramta wa shiga Amirka.

Hada karfi  da nufin yakar matakan Trump

Tutar Amirka da ta Kungiyar Tarayyar Turai, danganta na neman yin tsami
Tutar Amirka da ta Kungiyar Tarayyar Turai, danganta na neman yin tsamiHoto: Imago/Manngold

Ko da shi ke dai matakin bai shafi kasashen Turai kai tsaye ba, amma kuma Tarayyar Turai EU ta ce za ta yi tsayuwar daka don ganin cewar bai yi tasiri a kan 'ya'yanta ba. Ma'ana ba zata bari Amirka ta hana wa 'yan kasashe bakwai da ke rike fasfo din wata kasa ta Turai shiga Amirka ba. Wasu 'yan kasuwa na Sudan ciki har da Amer Hamed al-Manufi sun ci karo da matsala a filin jirgin sama a lokacin da suka yi kokarin shiga Amirka. Saboda haka ne gwamnatin ta Sudan ta bayyana fushinta a fili bayan da aka dawo da su. Ita ma Kungiyar Tarayyar Afirka AU karkashin sakatariyar zartaswa Nkosazana Dlamini-Zuma ta nuna mamaki game matakin na Trump tare da kira ga kasashen Afirka da su tashi tsaye domin su gudu tare su tsira tare. Ita dai dokar da ta jawo kace-nace ta haramta wa 'yan gudun hijira shiga Amirka na tsawon kwanaki 120. Sannan ta haramta wa 'yan kasashen Iran da Iraki da Libiya da Somaliya da Sudan da Siriya da Yemen shiga Amirka na tsawon kwanaki 90.