Martani kan sauyin gwamnati a Gambiya
December 4, 2016Kafin dai shugaba Yahya Jammeh ya fidda sanarwar amincewa da shan kaye, tsakiyar Banjul babban birin kasar Gambiya ya kasance wayam, kuma kumai tsit, domin babu wanda yan son mi zai biyo baya, kuma bisa sanin da aka yi wa Jammeh na takurawa 'yan adawa, babu wanda ya zaci zai amince ya sha kaye cikin ruwan sanyi,. Amma kwasom jiya Asabar sai aka ji shugaban na kasar Gambiya a kewaye da majalisar ministocinsa, ya fidda sanarwa ta gidan talabijin din kasar kamar haka.
"Ina son yin amfani da wannan dama don na taya murna ga Mr Adama Barrow, bisa nasarar da ya yi. Nasara ce ta zahiri, saboda dokar kasarmu ta ce, ga duk wanda ya yi rinjaye ko mi karanshinsa. Na karbi mulkin kasar nan ne a ranar Jumma'a 22 ga watan Julin shekara ta 1994, kuma a wannan Jumma'a biyu ga watan Disamba, 'yan kasar Gambiya sun yanke shawara na koma bayan kujerar mulki. Na yarda zan sauka, don kare kasar mu, kuma zan yi amfani da sanayyar da na ke da ita don taimaka wa sabon shugaba Adama Barrow ya karbi mulki, yayinda ni kuma, zan tattara nawa na koma gona"
Yada wannan sanarwar ke da wuya, sai jama'ar Gambiya suka fantsama kan titi da murna. Shi kansa shugaban kasar Gambiya mai jiran gado Adama Barrow, nasarar da ya yi, da amincewar Yahya Jammeh ta zo masa ba zata. Kamar yadda ya bayyana.
"Ina cike da farin ciki, domin kowa yana ganin ba abune mai samuwa ba. Amma abu mai yuwa sai gashi ya zama mai sauki. Wannan ya saka mu cikin farin ciki. Ina ganin mun yi aiki mai yawa kafin mu kai ga hakan".
Ba tare da bata lokaci ba sabon shugaban kasar ta Gambiya, Adama Barrow, ya bayyana manyan ayyukan da ke gabansa da zaran ya karbi mulki.
"Fursunonin siyasa za'a sake su, idan dai bisa siyasa aka daure ka, to ka saku. 'Yan kasar Gambiya da ke waje ana maraba da su, kai tun sanar da sakamakon zabe, ina ganin an cire musu takunkumin dawowa gida. Muna maraba da duk dan kasar mu da ke waje, da yardan Allah zamu gina kasarmu tare, 'yan kasamu da ke waje sun bada gudumawa mai yawa, sun bada kudinsu da shawarwari don tabbatar da nasar mu"
A kan batun ficewar kasar Gambiya daga Kotun ICC mai hukunta manyan laifuka na kasa da kasa, Barrow ya ce Gambiya za ta koma ciki.
"Idan muka karbi mulki za mu dakatar da batun ficewar nan take, domin ICC na kare mulkin mai kyau ne, kuma in kana mulkin mai kyau, bai kamata ka fice daga ICC ba"
Wannan amincewar da Yahya Jammeh ya yi na shan kaye, ya baiwa mutane daga ciki da wajen kasar ta Gambiya mamaki, ganin irin mulkin kama karya da ake zargin ya yi cikin shekaru 22. Don haka tuni aka fara yaba Jammeh, kamar yadda aka ji dan takara na uku a zaben kasar ta Gambiya Mamma Kandeh na cewa.
"Tsoron mu ada shi ne, ko shugaba Jammeh ba zai mika mulki ba, kuma ba zai amince da shan kaye ba. Don haka ina son taya Jammeh murna, domin ya bai wa dukkan duniya mamaki, ganin ba wanda ya zaci shugaban zai mika mulki, ko ya amince da shan kaye cikin lumana. Wannan ya bude kekkewan babi ga rayuwar kasar Gambiya. 'Yan kasar sun yi magana, kuma Gambiyawa kansu a hade yake"
Yahya Jammeh ya hau mulkin 'yar mistitsiyar kasar Gambiya a shekara ta 1994, bayan juyin mulkin da ya yi wa tsohon shugaban kasar Dawda Jawara, inda daga baya ya tobe kaki soje ya tsaya takara a shekara ta 1996. Kuma Jammeh bai rage wa duk mai adawa da shi, a tsawon shekarun 22 da ya yi yana mulki. Amma sai kuma bisa ga dukkan alamu zai mika mulkin cikin lumana bisa tsarin demokradiyya.