1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan takarar shugaba Jonathan a 2015

Uwais Abubakar IdrisOctober 24, 2014

Takarar da shugaban Najeriya ya ce zai yi a 2015 ta haifara da maida martani daga bangarori daban-daban na kasar kan halarci ko akasin haka.

https://p.dw.com/p/1Dbl4
Nigeria Präsident Goodluck Ebele Jonathan in Brüssels
Hoto: picture-alliance/dpa

Bayyana aniyarsa ta shiga zabukan 2015 da shugaban Najeriya ya yi yanzu haka dai ya kawo karshen halin rashin tabbas da ya bar al'ummar kasar ciki. Wannan mataki nasa dai ya kara bude babi na muhawarar da ake yi game da irin tanadin da kundin tsarin mulkin kasar ya yi na wa'adin da ya kamata shugaba ya yi a gadon mulki.

Nigerias Terror geht weiter
Jam'iyyar PDP na kokarin baje kolin irin aiyyukan da ta yi don samun kuri'u a 2015Hoto: DW/K. Gänsler

Tuni dai masu sharhi kan lamura na siyasa da ma sauran al'amuran yau da kullum a Najeriya ke bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta kan wannan batu, yayin da wasu 'yan siyasa a nasu bangaren ke cewar ba za ta sabu ba domin yin takarar tasa tamkar halarata abinda ya ke haramun ne.

Dr. Sadeeq Umar Abubakar darakta na gamayyar hada kan jam'iyyun kasar na daga cikin masu adawa da wannan takara ta shugaban Najeriya inda ya ce dalilinsu na yi adawa da takarar Jonathan bai da nasaba da siyasa, kokari ne a cewarsa na ganin an bin dokokin kasa sau da kafa.

A share guda kuma wasu 'yan kasar ciki kuwa har da wanda ke cikin wasu jam'iyyun siyasa sun ruga kotun don ganin Shugaba Jonathan bai kai ga yin takarar ba, sai dai a hannu guda Alhaji Isa Tafida Mafindi wakili a kwamitin zartaswar jamiyar ta PDP na ganin takarar ta shugaba Jonathan na kan ka'ida hasali ma a cewarsa masana harkokin shari'a sun ce shugaban zai iya yin takara don hakan bai sabawa doka ba.

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Jam'iyyun adawa na cigaba da korafi dangane da gaza tabuka abin kirki da gwamnatin PDP ta yi.Hoto: Atiku Media Office

Da alamu dai yanzu hankula za su karkata zuwa kotunan Najeriyar inda a can ne za a rarrabe danagne da wannan takaddama tsakanin jam'iyyun adawa da ke hangen babu hallaci ga sake sayawa takara ta Jonathan da kuma jam'iyyarsa ta PDP.