Martanin Isra'ila kan karɓar Falisɗinu a UNESCO
November 2, 2011Mahukuntan Falisɗinu sun nuna rashin amincewarsu da shawarar da Isra'ila ta tsayar ta gina sabbin matsugunai dubu biyu a gabashin birnin Ƙudus da Gaɓar yamma da kogin Jordan. Kakakin shugaban Falisɗinawa, Mahmoud Abbas ya ce wannan shawara wata aba ce da ka iya kawo cikas ga tafarkin samar da zaman lafiya. Ko a ranar talata 2.11.2011 sai da Isra'ila ta sanar da dakatar da tura kuɗaɗen haraji ga mahukuntan Falisɗinu. Kamar dai yadda aka saba Isra'ila ta kan tura kuɗaɗen haraji da take karɓa a madadin Falisɗinawa.
Isra'ila ta ɗau wannan mataki ne bayan da hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da Falisɗinu a matsayin manbanta- matakin da ya ɓata ran Isra'ila da Amirka da kuma Jamus. Ana san ran Amirka zata hau kujerar na ki a lokacin da komitin sulhu na majalisar dinkin duniya zai kada kuria akan yunkurin Falisdinawa na samun kujerar a majalisar dinkin duniya a wata mai zuwa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu