1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kasashe akan gwajin makamin nuclearn koriya ta arewa

Zainab A MohammedOctober 13, 2006
https://p.dw.com/p/Btxl
Jonh Bolton,jakadan Amurka a mdd
Jonh Bolton,jakadan Amurka a mddHoto: AP

Kasashen duniya naciga da tofa albarkacin bakinsu,a matsayin martani kan sanarwar gwajin makamin Nuclear da kasar Koriya ta arewa tayi,adaidai lokacin da komitin sulhu ke laakari da kakaba mata takunkumi,amma banda amfani da karfin soji akanta.

Sabon tsarin da kwararrun komitin suka rubuta ,bayan zartarwar jakadun kasashe membobi akan muhimman batutuwa,ya kunshi matakan kakaba mata takunkumi da suka hadar da na tattalin arziki,da yanke diplomasiya da Koriya ta arewan,amma banda amfani da karfin Soji.

Kasar Sin dake zama babbar abokiyar Koriyan,kuma daya daga cikin kasashe masu zaunanniyar kujera a komitin sulhun,nada matukar tasiri adangane da kowane mataki zaa dauka na ladabtar da koriya ta arewa,adangane da sanarwar gwajin makamin nuclearn datayi a ranar litinin.

Wannan sabon tsarin kudurin wanda aka bawa yan jarida ayau,ya kumayi Allah wadan gwajin ,wanda ke zama watsi da gargadin komitin sulhu a bangaren koriyan.

Jakadan Amurka a mdd John Bolton ya fadawa manema labaru cewa,bazaiyi gaggawan fadin cewa sun cimma yarjejeniyata ta bai daya ba,amma sun cimma daidaituwa akan muhimman batutuwa.

Kasashen Sin da dai da Koriya ta kudu dai sun nuna amincewarsu adangane da kowane mataki da zaa dauka na ladabtar da Pyongyang kan gwajin makaminta.

A tattaunawarsu ta hadin gwiwa,inda batun koriya ta arewan ya mamaye,shugaba Hu Jintao da takwaransa na koriya ta kudu Roh Moo-hyun dake ziyarar aiki a Beijing,sunyi Allah wadan gwajin,sai dai basu tabo batun tsarin kudurin da Amurka ta gabatar,wanda yayi bayanan matakan takunkumi kan Pyongyang ba.

Mai bawa shugaban Koriya ta arewa shawara kan harkokin tsaro Song Min-soon yace shugabannin biyu sun amince da bada hadin kansu wa kowane mataki komitin sulhun mdd ya zartar kan koriya ta arewa.

Ayau ne yan majalisar zartarwan Japan suka zartar da kudurin rufe dukkan tashoshin jiragen ruwan kasar wa jiragen koriya ta arewa,tare da haramta duk wata dangantakar ciniki da ita.

Premiern Japan Shinzo Abe yayi fatan cewa wannan takunkumi da kasarsa ta kakabawa Koriyan ,zai yi tasiri wajen durkusar da ita.

Gwamnatin Tokyo ta dauki wadannan matakai na hukunta Koriyan ne,duk dacewa har yanzu babu tabbaci dangane da gwajin makamin nuclearn data sanar.

To sai dai shugaban hukumar gudanarwa na EU Jose Manuel Borosso ,yace yadda duniya ta mayar da martani kan sanarwar gwajin makamin na koriya ta arewa,na matukar barazana ga zaman takewa.

Ayayinda ita kuwa asusun kula da yara ta mdd watau UNICEF,gargadi tayi adangane dacewa,kowane irin matakin hukunci zaa dora akan koriya ta arewa kada ya shafi rayuwar yaran kasar.Kakakin hukumar Michael Borciukiw,ya jaddada muhimmancin laakari da makomar yaran kasar,adangane da kowane takunkumi zaa dora mata.