Martanin sakin tsaffin gwamnonin Najeriya
August 9, 2022Bayan sakin tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye daga gidan yari, jama'ar Filato na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta dangane da sakin tsohon gwamnan wanda ake zargi da laifin sace kudin jama'ar lokacin da yake kujerar gwamnan jihar.
Tun dai a ranar 14th, ga watan Afrilu na wannan shekarar ce majalisar koli ta tarayyar Najeriya ta yi ahuwa ga wasu 'yan Najeriya 159, ciki har da tsaffin gwamnoni biyu, Jolly Nyame na jihar Taraba tare da Joshua Dariye na jihar Filato. To sai dai tun wancan lokaci fa wasu jama'a 'yan Najeriya suka soma nuna shakku ga ikirarin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na yaki da cin hanci da rashawa.
A jihar Filato dai tun bayan fitowar tsohion gwamna Dariye daga gidan yarin Kuje, wasu jama'ar jihar musaman 'yan asalin karamar hukumar Bokkos maihaifar Dariye, suke ta bukukuwa.
To amma ga Madam Ladi wata 'yar gwagwarmaya sakin Dariye rashin adalci ne wa duk 'yan Najeriya da ke tsare da suka aikata kananan laifuka.
Wasu al'ummar jihar Filato da wakilinmu ya zanta da su na gani cewar sakin tsohon gwamnan bai kamata ba, don kuwa a lokacin gwamnatinsa ne jihar Filato ta fuskanci tashe-tashen hankula a shekarun baya, wasu kuwa cewa suke sakin Joshua Dariye lamari ne daya chanchanta sakamakon halin da ya shiga, yayin da kuma wasu ke daganta lsakin tsaffin gwamnonin biyu kan lamari na siyasa tsantsa.